Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 13:43:57    
Hukumar tanadin kundin tarihi ta kasar Sin ta bayar da wayar da Dalailama ya buga zuwa ga tsohon shugaban kasar Sin Mao Tsedong

cri

A ranar 7 ga wannan wata, hukumar tanadin kundin tarihi ta kasar Sin ta bayar da wata wayar da Dalailama na 14 ya buga ga tsohon shugaban kasar Sin Mao Tsedong dangane da lamarin nuna goyon baya ga wata yarjejeniya wadda aka tanada a cikin gidan tanadin kundin tarihi na tsakiya na kasar Sin. A cikin wayar, a bayyane ne Dalailama ya nuna goyon baya ga yarjejeniya kan dabarar da ake bi don 'yantar da Tibet cikin lumana, kuma ya bayyana cewa, a karkashin shugabancin shugaba Mao da gwamnatin tsakiya, ana kiyaye dayantaccen ikon mallakar cikakken yankin kasar mahaifa.

A cikin wayar da Dalailama ya buga zuwa ga shugaba Mao Tsedong a watan Oktoba na shekarar 1951, an bayyana cewa, an daddale yarjejeniya kan dabarar 'yantar da Tbiet ne cikin lumana bisa tushen sada zumunta. Gwamnatin Tibet da mabiyan addinin Buddah na kabilar Tibet gaba daya ne suka nuna goyon bayansu gare ta, kuma a karkashin shugabancin shuagba Mao da gwamnatin tsakiya, sun ba da taimako cikin himma da kwazo ga rundunar sojan suncin kai ta jama'ar Sin da ke shiga Tibet da su inganta tsaron kasa da korar kungiyoyin kasashe masu nuna fin karfi da kuma kiyaye ikon mallakar dayantaciyyar kasa da cickakken yankin kasa.(Halima)