Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 10:55:10    
'Yan kallon kasashen ketare sun mai da hankali ga labaran da gidan rediyo mai hoto na tsakiya na kasar Sin wato CCTV ya bayar kan lamarin Tibet

cri
Bayan aukuwar lamarin duka da kwace da fashi da kuma kone kayayyaki a ranar 14 ga watan Maris a birnin Lhasa, labaran da suka shafi lamarin Tibet a gidan rediyo mai hoto na tsakiya na kasar Sin wato CCTV sun jawo hankulan 'yan kallon kasashen ketare sosai. 'yan kallo da yawa sun buga waya ga gidan CCTV cewa, wadannan shirye-shiryen musamman sun karyatar da labaran da kafofin yada labarai na kasashen yamma suka bayar ba cikin gaskiya ba, sun kuma shaida cewa, tun zamani aru aru, Tibet ita ce yankin kasar Sin, an kuma tono danyen aikin da rukunin Dalai ya yi na kawo wa kasar mahaifa baraka.

Wani dan kallo na kasar Philipings Mr Rim ya bayyana cewa, daga cikin shirye-shiryen cannel-9 na CCTV, na yi bakin ciki da ganin wasu jama'ar farar hula suka mutu a yayin da wasunsu suka ji raunuka a cikin lamarin duka da kwace da fashi da kuma kone kayayyaki, ya kamata a yi wa wadannan masu yin laifufuka ba bisa doka ba hukunci mai tsanani.

Wani dan kallo na kasar Faransa Mr Jean Sebastien Shawia ya buga waya zuwa ga channel na harshen Faransa na CCTV cewa, bayan da na kallaci labaran da kuka bayar dangane da lamarin nuna karfin Tuwo a Tibet, sai na kara amince da hakikanan abubuwa da ra'ayin da manema labarunku suka bayyana, a ganina, wannan ne na da gaskiya. Wata 'yar kallo ta kasar Faransa mai suna Sun Xiaohua ta buga waya ga channel na kasa da kasa da aka yi shirye-shirye da harshen Faransa na CCTV cewa, hotunan da kuka dauka sun maido da hakikanan abubuwa, abubuwan da kuka bayar wa jama'ar kasar Faransa abubuwa ne na gaskiya.

Dan kallo na kasar Amurka mai suna Zheng Zijie ya buga wayar telephone cewa, lamarin duka da kwace da fashi da kuma kone kayayyaki da aka yi da karfin tuwo a birnin Lhasa su ne aikace-aikacen haddasa barna da rukunin Dalai ya yi a bayyane , makasudinsa shi ne don kawo barna ga wasannin Olimpic na Beijing da kuma kawo wa al'umma barna, Sinawanmu da ke zama a kasashen ketare sun yi fushi sosai a kai.

Dan kallo na kasar Norway mai suan Yingming ya bayyana cewa, mun tsayawa tsayin daka da amince cewa, jama'ar Tibet ba za su iya yarda da koma zamantakewar al'umma mai aiwatar da mulkin bayi manoma, kuma makircin da rukunin Dalai ya yi ba zai ci nasara ba, kowane mutum zai bi ruwa wajen aikinsa na balle Tibet daga kasar mahaifa.(Halima)