Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 21:43:14    
Kawo cikas ga mika wutar wasannin Olympics da wasu tsirarrun 'yan awaren Tibet suka yi bai sami karbuwa ba, in ji kwamitin kula da wasannin Olympics na Beijing

cri
A gun taron sanar da yadda ake gudanar da aikin mika wutar wasannin Olympics na Beijing da aka yi yau a nan birnin Beijing, shugabar sashen watsa labarai na kwamitin kula da wasannin Olympics na Beijing, Madam Wang Hui ta bayyana cewa, kawo cikas ga aikin mika wutar wasannin Olympics da wasu 'yan tsirarrun 'yan awaren Tibet suka yi bai sami karbuwa ba.

Madam Wang Hui ta ce, a lokacin da ake mika wutar wasannin Olympics na Beijing, wasu tsirarrun 'yan awaren Tibet sun kawo cikas ga aikin. A yayin da ake mika wutar yola a birnin London, sau da dama wasu 'yan awaren Tibet suka ketare kawanyar da 'yan sanda suka yi. 'Yan sandan Birtaniya sun kama wasu 'yan awaren Tibet wadanda suka kawo barnar.

Ta ce, wutar wasannin Olympics wuta ce ta jama'ar duniya baki daya, tsokanar manufar wasannin Olympics da wasu tsirarrun mutane suka yi bai sami karbuwa ba, kuma ba shakka, zai fusatar da jama'ar da ke kishin zaman lafiya da goyon bayan manufar, kuma tabbas ne tsirarrun mutanne za su sha kashi a yunkurinsu.(Lubabatu)