Tare da komar da oda yadda ya kamata a birnin Lhasa, an sake bude kofar wuraren al'adu da nishadi ga jama'a, wadannan na'urori an rufe su ne sakamakon lamarin da ya faru a ranar 14 ga watan jiya.
Ran 6 ga wata, ranar Asabar, wakilimmu ya shiga cikin dakin nune nune na jihar Tibet, ya ga yawan mutanen da suke ziyara a dakin ya karu zuwa matsayin yadda ya kamata. A dakin littattafai na birnin Lhasa, jama'a suna zaune a gaban tebur, suna karatu cikin kwanciyar hankali. A cikin wani shahararren dakin motsa jiki na birnin Lhasa, wasu 'yan mata suna yin wasan lankwashe jiki. A gabansu kuma, matasa da yawa suna liftin .
Da dare ya yi, jama'ar Tibet sun fara zaman rayuwa da dare kamar yadda suke yi a da.(Danladi)
|