Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 20:43:45    
Beijing zai shirya wani gaggarumin wasannin Olympic, a cewar jami'an kwamitin wasannin Olympic na duniya

cri
'Dan kwamitin wasannin Olympic na duniya Kevan Gosper, ya bayyana a yau 7 ga wata a nan birnin Beijing cewa, birnin Beijing zai shirya wani gaggarumin wasannin Olympic ga duniya.

Mr. Gosper ya dare kujerar mataimakin shugaban hukumar daidaitawa ta wasannin Olympic a karo na 29 ta kwamitin wasannin Olympic na duniya, a gun babban taron wakilai kan ayyukan daidaitawa na duniya a karo na 16 da aka bude a yau, Mr. Gosper ya gabatar da cewa, kwamitin daidaitawar ya kawo karshen bincike kan ayyukan share fage na wasannin Olympic na Beijing a makon da ya wuce, kuma ya nuna gamsuwa sosai kan ayyukan da kwamitin Olympic na Beijing ya yi.

Mr. Gosper ya ce, dakuna da filaye na wasannin Olympic na Beijing suna da kyau, kuma birnin Beijing ya riga ya bayar da kudi dalar Amurka biliyan 1.5, don kyautata ingancin iska. Saboda haka, dukkan maganganun da aka yi kan cewar, wai iskar birnin Beijing za ta kawo illa ga lafiyar jikunan 'yan wasa, ba gaskiya ba ne.

Bugu da kari kuma, a lokacin da manema labaru suka kai masa ziyara don jin ta bakinsa, shugaban hukumar daidaitawa ta wasannin Olympic a karo na 29 ta kwamitin wasannin Olympic Hein Verbruggen shi ma ya nuna gamsuwa sosai ga ayyukan share fage kan wasannin Olympic na Beijing. (Bilkisu)