Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ta tsaya kan bunkasa sana'o'i masu halayen musamman na faffadan tsauni ciki har da aikin noma da kiwon dabbobi da yawon shakatawa, ta yadda wadannan sana'o'i suka zama wani sabon tashe wajen bunkasa tattalin arzikin jihar.
An ce, cikin kusan shekaru 5 da suka wuce, jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta ware kudin Sin da yawansu ya kai fiye da Yuan biliyan daya domin tallafa da kuma bunkasa ayyuka kusan 200 masu halayen musamman wajen noma da kiwo , sabo da haka an kara samun ci gaba da sauri wajen gudanar da ayyukan noma da kiwo. Ban da wannan kuma bisa taimakon da gwamnati ta bayar, sana'ar yawon shakatawa tana ta zama wata sana'ar ginshiki ga tattalin arzikin jihar Tibet.
Ban da wannan kuma, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sana'ar yin magungunan jihar Tibet da sana'ar yin abinci masu inganci, da kuma sana'ar hannu na kabilar Tibet da sauran sana'o'i masu halayen musamman na jihar Tibet su ma suna ta samun bunkasuwa mai kyau. (Umaru)
|