Ran 6 ga wata, yan sanda na kasar Birtaniya sun kama wasu kalilan mutane masu "neman 'yancin Tibet" wadanda suka nufin bata aikin mika wutar wasannin Olympics na Beijing. Game da laifuffukan da suka yi, mazauan da ke wurin sun yi fushi sosai.
A wannan rana da safe bisa agogon wurin, an fara mika wutar yola ta wasannin Olympics na Beijing cikin farin ciki da ban tafi da ake yi. Yayin da ake mika wutar yola, bi da bi ne wasu kalilan mutane masu "neman 'yancin Tibet" sun yi kokari bata aikin mikawa, amma nan da nan bangaren 'yan sanda na kasar Birtaniya suka kama su, haka kuma ana cigaba da mika wutar yola yadda ya kamata. Game da haka, kakakin cibiyar mika wutar yola ta kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya yi kakkausar suka. Ya yi nuni da cewa, wutar yola ta jama'ar dukkan kasashen duniya ce, wasu kalilan mutane sun yi aikin tada fitina ga ainihin wasannin Olympics a gaban jama'a, ba za su sami goyon baya ba, kuma za su sami adawar mutanen da suke goyon baya zaman lafiya da ainihin wasannin Olympics.
|