Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 15:17:08    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- A ran 14 ga wata, hukumar kula da zaman lafiya ta birnin Urumchi, hedkwatar jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke yammacin kasar Sin ta fayyace cewa, yanzu hukumar 'yan sanda ta wannan birni ta riga ta dauki matakai domin ba da tabbaci ga bikin bai wa juna wutar yula ta wasannin Olimpic da kuma gudanar aikin kiyaye kwanciyar hankali yadda ya kamata a lokacin wasannin Olimpic.

Mr. Chen Zhuangwei, shugaban hukumar kula da zaman lafiya ta birnin Urumchi ya bayyana cewa, za a kara rubanya kokari wajen murkushewa da yin rigakafi sosai kan "munanan abubuwa iri 3" wato ta'addanci da ra'ayin jawo baraka da kuma masu tsattsauran ra'ayi. Za a tsaya-tsayin daka wajen murkushe dukkan waddanda suka kuskura suka yi kulle-kullen ta'addanci da kawo barazana ga wasannin Olimpic, ta yadda za a kawar ka dukkan miyagun abubuwa da za su jawo illa ga zaman lafiyar wasannin Olimpic tun farkon fitowarsu.

---- A ran 19 ga wata, gwamnatin gundumar Tianyang ta birnin Baise na jihar Guangxi ta kasar Sin, wurin da aka haifar da al'adun Buluotuo na kabilar Zhuang ta sanar da cewa, daga ran 12 zuwa 13 ga watan Afril mai zuwa, za a shirya bikin yawon shakatawa na al'adun Buluotuo na kabilar Zhuang na shekarar 2008 a wannan gunduma.

A gun wannan bikin yawon shakatawa na al'adu, za a shirya bukukuwa daban-daban, ciki har da shagalin dare na Buluotuo, da bikin yin addu'a domin tunawa da Buluotuo, da rera wakokin tudu tsakanin rukunoni 2, da nuna abincin gargajiya masu dadi na kabilar Zhuang, da wasa da zaki, daga cikin su kuma bikin shagalin dare na Buluotuo ya fi jawo hankulan mutane.

Bisa bayanin da Mr. Zhang Zhijie, mataimakin shugaban gundumar Tianyang ya bayar an ce, bikin shagalin dare na Buluotuo da za a yi a wannan shekara yana da sigar musamman na al'adun gargajiya da na wurin kabilar, a gun bikin za a bayyana kyawawan halayen kabilu da al'adun gargajiya masu dogon tarihi a mahaifar Buluotuo. Ban da wannan kuma za yi wasan karon shanu da sauran wasannin motsa jiki.

Kabilar Zhuang tana da mutane fiye da miliyan 10, wato ita ce ta fi yawan mutane daga cikin kananan kabilun kasar Sin, kuma yawancinsu suna zama cikin jihar Guangxi ne ta kasar Sin. Ya zuwa yanzu an riga an yi bikin yawon shakatawa na al'adun Buluotuo har sau 4 tare da nasara.(Umaru)