Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 15:07:24    
Mr Hans Loontiens, babban majanan hotel mai matsayin taurari biyar a birnin Tianjin na kasar Sin

cri

A cikin shekarun nan da suka wuce, an bunkasa yankin raya tattalin arziki da fasaha na birnin Tianjin na kasar Sin wato TEDA cikin sauri. Wannan ya samar da sabuwar dama domin bunkasa harkokin otel-otel a yankin TEDA. Daga cikin otel-otel da aka gina a yankin, Hotel din Wanliteda mai matsayin taurari biyar shi ne mafi girma, Mr Hans Loontiens, dan kasar Belgium kuma ya zama babban manajan wannan hotel.

Kafin zuwansa a birnin Tianjin, Mr Hans Loontiens babban manajan wani hotel din kasar Masar ne. An turo shi zuwa birnin Tianjing ne a watan Nuwamba na shekarar bara domin aiki. Bayan da ya sami sanarwar aikinsa, sai ya fara neman duk bayanai a kan birnin Tianjin da TEDA ta hanyar Internet. Sa'an nan ya nuna cikakken imaninsa ga sabon aikin da zai yi. Hausawa na cewa, gani ya kori ji. Bayan saukarsa a yankin raya tattalin arziki da fasaha na birnin Tianjin wato TEDA, sai nan da nan ya gano cewa, "hukumomi suna dora muhimmanci sosai ga raya yankin TEDA. Na yi matukar farin ciki da samun damar yin aiki a irin wannan yankin da ke samun bunkasuwa cikin sauri. A ganina, zaman babban manajan hotel a wani yankin da ake bunkasa harkokin otel-otel cikin sauri wani aiki ne mai kyau sosai ga rayuwar mutane. "

Yanzu, yankin TEDA ya riga ya zama yanki mafi girma a birnin Tianjin wanda ke ma'amala a tsakanin Sin da kasashen waje. Akwai bakin da suka fito daga kasashe da shiyyoyi 33 da ke zama da aiki a yankin TEDA har cikin dogon lokaci. Yanzu sun riga sun saba da zaman rayuwarsu sannu a hankali, kuma sun zama jama'a da magina a yankin. A hakika dai, Hans Loontiens ya taba shafe sama da shekaru 10 yana aiki a birnin Shanghai da sauran wurare na kasar Sin, sabo da haka kasar Sin ba wani bakon abu ne gare shi ba. Da ya tabo magana a kan zamansa a yankin TEDA, sai ya bayyana cewa, "a lokacin da nake zama a kasar Sin yau sama da shekaru 20 da suka wuce, zaman rayuwarmu ba shi da sauki, baki na kasashen ketare ba su iya samun kayayyaki da yawa da suke bukata a cikin kasuwanni ba. Amma yanzu manyan kantuna suna sayar da kayayyaki iri daban daban da baki na kasashen ketare ke bukata. A da, idan wani bako ya zo kasar Sin daga kasashen waje don yin zama da aiki, wajibi ne, ya dauko kayayyakin masarufi da yawa a cikin akwatinsa, amma yanzu ba haka suke yi ba." Mr Hans Loontiens ya kara da cewa, ko da yake bai dade yana aiki a birnin Tianjin ba, amma yana nuna aminci sosai ga kasar Sin. Uwargidansa ita ce wata kyakkyawar mace da ta fito daga birnin Shanghai na kasar Sin. Ya tarar da matarsa ne yayin da yake aiki a birnin Shanghai yau da shekaru 23 da suka wuce. Ya zuwa yanzu sun daura aurensu ne har cikin shekaru 21 da suka wuce. Bayan aurensu, sun yi zamansu a birnin Shanghai a cikin shekaru da dama. Bisa goyon baya da fahimta da matarsa ta nuna, Mr Loontiens ya gano kyakkyawan hali na mata na kasar Sin. Ya ce, "mata Sinawa nagartattu ne. Suna son karbuwar sabbin abubuwa da sabbin sauye-sauye. Amma ba dukkan mata na ko wace kasa ke iya yin haka ba. Idan wani mutum ya so ya yi aiki da kyau sosai, to, dole ne, ya sami goyon baya daga wajen iyalinsa, sai ta haka dai ne zai iya yin iyakacin kokari wajen yin aikinsa."

Bisa al'adar gargajiyar kasar Sin, bera ya zama alamar wannan shekara. Jama'ar Sin kuma suna kiran shekarar nan da sunan shekarar zinariya, abin da ake nufi shekarar zinariya shi ne kawo alheri ga jama'a. A karshen lokacin zayarar da wakilin rediyonmu ya kai masa, Mr Hans Loontiens ya ce, yana fatan zai ciyar da aikinsa gaba. Kuma yana fatan jama'a masu sauraronmu za su gudanar da harkokinsu lami lafiya. (Halilu)