Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 14:53:17    
Kada wasu 'yan majalisa na kasar Amurka su bata huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka a cewar Jiang Yu

cri

Ran 7 ga wata a nan birnin Beijing, Madam Jiang Yu kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta nuna cewa, kasar Sin ta ba da shawara ga wasu 'yan majalisa na kasar Amurka da su girmama abin gaskiya, kuma su daina nuna bambanci, da kokarin fahimtar asalin rukunin Dalai Lama, kuma kada su yi kokarin gabatar da kudurin yin shawarwari kan batun Tibet, kada su bata zuciyar jama'ar kasar Sin da huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka.

A kwanakin baya, Mr. Pelosi shugaban majalisar dokoki ta kasar Amurka ya gabatar da kuduri, inda ya yi kira ga gwamnatin kasar Sin da ta daina yin wai danniya a jihar Tibet, kuma ta yi shawarwari tare da Dalai Lama a zahiri. Game da haka, Madam Jiang Yu ta nuna cewa, kudurin da wasu kalilan 'yan majalisa na kasar Amurka suka gabata ba su yi suka ga mutane masu tada manyan laifuffuka masu tsanani sosai a birnin Lhasa, ba su suka ga rukunin Dalai Lama wanda ya shirya aikace-aikaci masu laifuffuka da gangan a boye, maimakon haka sun zargi gwamnati da jama'ar kasar Sin, wannan ya kawo rudani tsakanin gaskiya da karya, tare da mugun nufi.

Madam Jiang Yu ta ce, idan Dalai Lama ya yi watsi da ra'ayin "neman 'yancin kan Tibet", daina neman ballewar kasar Sin, da daina shirya al'amarin tada manyan laifuffuka da bata wasannin Olympics na Beijing, kuma ya yarda da Tibet da Taiwan su ne wani yanki na kasar Sin wadanda ba za a iya bellewa ba, gwamnatin tsakiyar kasar Sin za ta son cigaba da yin shawarwari tare da shi.