Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 13:25:49    
Manyan jami'an kwamitin IOC da kasashen duniya da yawa sun nuna adawa da kaurace wa wasannin Olympcis na Beijing

cri

A kwanakin baya, manyan jami'an kwamitin IOC da na wasu kasashen duniya da yawa sun yi jawabi, da sharhi, da sanarwa, inda suka nuna adawa da kaurace wa wasannin Olympics na Beijing.

Ran 5 ga wata a kasar Singapore Mr. Rogge shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya wato kwamitin IOC ya jaddada cewa, a mayar da ikon yin wasannin Olympics ga birnin Beijing wani zabi mai basira, kwamitin IOC ba za ta yi da-na-sani ba. Kuma ya yabawa aikin shirya da kwamitin shiryawa wasannin Olympics ya Beijing ta yi.

A ran 3 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Verbruggen shugaban hukumar tsare-tsaren wasannin Olympics na Beijing na karo na 29 ta kwamitin IOC ya yi wani sharhi, inda ya nuna adawa da a mayar da harkokin siyasa kan wasanin Olympics na Beijing. Ya yi nuni da cewa, ya kamata a ba da wasannin Olympics ga 'yan wasa, ba 'yan siyasa ba.

A ran 2 ga wata, Mr. Samaranch shugaba mai mukamin girmamawa na kwamitin IOC ya ce, batun Tibet shi ne wani lamarin siyasa, "babu ruwan wasannin motsa jiki ba ko kadan", kwamitin IOC shi ne "wata hukumar wasan motsa jiki, ba ya iya sa hannu kan sauran fannoni".

A ran 5 ga wata, Mr. Jowell jami'I mai kula da harkokin wasannin Olympics na kasar Birtaniya ya ce, ko shakka babu gwamnatin kasar Birtaniya ba za ta kaurace wa wasannin Olympics na Beijing ba.

Ran 2 ga wata a Paris, babban birnin kasar Faransa, Mr. Lamour tsohon ministan harkokin motsa jiki na kasar ya ce, mutane da yawa ba su san Tibet sosai ba, idan saboda haka su kaurace wa wasannin Olympics na Beijing, ba shakka za su yi kuskure.

Ban da haka kuma, sauran manyan jami'ai na wasu kasashe sun nuna adawa da kaurace wa wasannin Olympics na Beijing.