
A ran 6 ga wata da karfe 11 da minti 50 da dare bisa agogon wuri, jirgin saman musamman mai daukar wutar wasannin Olympic na Beijing ya isa filin saukar jiragen sama mai sunan Charles de Gaulle dake birnin Paris.
Jami'an kwamitin wasannin Olympic na Faransa da gwamnatin birnin Paris da kuma ofishin jakadancin kasar Sin dake Faransa sun je wurin don maraba da wutar. Daga baya, tawagar wutar wasannin Olympic ta shiga cikin birnin Paris a karkashin kariyar motocin 'yan sanda.
Za a yi bikin mika wutar wasannin Olympic a zangon Paris a ran 7 ga wata da rana kan lebur na hawa daya na hasumiyar Eiffel. Tsawon hanyar mika wutar yula zai kai kilomita 28, masu mika wutar 79 na kasar Sin da na Faransa za su shiga ciki.(Lami)
|