Memban kwamitin watsa labaru na kwamitin shirya wasannin Olympic na kasa da kasa kuma mataimakin shugaban kungiyar manema labarun wasanni na kasar Sin Gao Dianmin ya fayyace a ran 6 ga wata a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin cewa, manema labaru dubu 20 za su zo kasar Sin domin neman labarun wasannin Olympic na Beijing, rabinsu wakilan gidajen TV ne da masu ba da tamako gare su. Yawan manema labarun babban yankin kasar Sin zai kai kimanin dari 3.
Gao Dianmin ya bayar da wannan labari ne a yayin da ya ba da lacca a jerin kos din wasannin Olympic a birnin Shanghai cewa, a karo na farko ne kwamitin wasannin Olympic ya sayar da ikon ba da shirye-shiryen wasannin Olympic ta Internet a gun wasannin Olympic na Beijing, tashar internet ta gidan TV ta kasar Sin da wata tashar internet ta Australia sun samu ikon a karshe. Ban da wannan kuma, a gun wasannin Olympic na Beijing, 'yan wasanni sun iya shirya Blog nasu, wannan shi ne karo na farko a cikin tarihin wasannin Olympic.(Lami)
|