Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 12:47:51    
An karyata labarin da gungun Dalai Lama suka baza na cewa wai sojoji sun shiga rigar masu bin addin Lama

cri

A ran 6 ga wata, kamfanin dillancin labarai na Hsinhua,wato kamfanin dillancin labarai mafi girma a kasar Sin ya bayar da wanisharhi,inda ya bayyana cewa yayin da mutanen kasar Sin maza da mata,ciki har da mutanen Tibet, ke la'antar tashin hankalin da gungun Dalai Lama suka tayar a birnin Lhasa a ran 14 ga watan Maris,gungun Dalai Lama ya fitar da wani rahoto na cewa hoto ne na wasu sojojin da suka shiga rigar masu bin addinin Lama, ya kuma shafa bakin fanti ga sojojin Sin wai su kansu ne suka tayar da tashin hankali na birnin Lhasa.Mutanen dake cikin hoton yanzu sun fito fili sun karyata labarin da Gungun Dalai Lama ya baza.

Bisa gaskiya ,hoton da gungun Dalai Lama ya yi ikirarin cewa hoton sojoji masu shiga rigar masu addinin Lama, hoton ne da aka dauka yau shekaru shida ke nan yayin da ake daukar sinima " Almarar Tianmei",a lokacin wasu hafsoshi da mayaka suka shigar rigar masu bin addini domin shirya sinima.

Sojoji biyu da ke cikin hoton sun tabbatar da cewa an dauki wannan hoto ne yayin da suka shiga rigar masu bin addini domin shirya sinina. Domin rigunan da suka sa a wannan lokaci babu alamun da aka sa a jiki kuma babu tambarin kafada.Tun daga watan Mayu na shekara ta 2004, sojoji 'yan sanada suna da alamu bai daya a duk kasa.

Bayanin ya yi nuni da cewa "tsohon hoto" bai kulla kome bai illa ya kara bayyana mugun hali na gungun Dalai Lama a gaban kafofin yada labarai da kuma bayyana makircin da ya kan yi amfani da shi wajen kirkiro karya.(Ali)