Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 12:45:45    
  Ko kusa ba a lamuntar da tashin hankali a kasa mai bin dokoki

cri

A ran 7 ga wata, jaridar People's Daily ta kasar Sin,jarida mafi samun kwarjini a kasar Sin ta buga wani bayani mai sharhi wanda ya ke da lakabi haka:" ko kusa ba a lamuntar da tashin hankali a kasa mai bin dokoki."

Bayanin ya yi nuni da cewa tun daga ran 14 ga watan Maris, tsirarrun 'yan takife sun afkawa jama'ar da ba su ji ba su gani ba a birnin Lhasa da sauran wurare na jihar Tibet mai cin gashin kanta, batun nan ya girgiza hankulan mutanen duniya. duk wanda ya ke da hankali ya fusata kan miyagun laifuffukan da 'yan takife suka aikata, sun kuma nuna juyayi ga jama'ar da suka sha azaba, kuma suna farin ciki kan matakan da gwamnatin ta dauka bisa dokoki.

Bayanin ya ce wani aikin da gungun Dalai ya kan yi shi ne yin watsi da dokoki da neman jawo baraka ta hanyar amfani da karfin tuwo, yayin da ake la'antar miyagun ayyukan da suka yi, sai gungun Dalai ya rufe fuskarsa ta neman jawo baraka da wai "zanga zangar lumana", ya murda tashin hankali da "arangama tsakanin kabilu", ya mai da makircin neman 'yancin Tibet kan hanyar daidaituwa, ya kuma mai da "damuwar siyasa" "damuwar al'adu", duk domin juyar da hankulan mutanen duniya.

Bayanin ya ce a gaban tarihi da ainihin abubuwa, gungun Dalai ya yi amfani da zaman lafiya domin rufe ainihin nufinsa na tayar da tashin hankali, da ya yi wasa da rubutu domin rufe ainihin nufinsa na jawo baraka, har ma ya yi bakin kokarin tabbatar da makircinsa na 'yancin kan Tibet ta hanyar ta da fitina tsakanin kabilu, kome da ya yi kamar ya dauki dutse sama daga baya dutsen ya fadi kan kafafuwansa.(Ali)