Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 11:01:46    
Yawan kudaden da jihar Tibet za ta zuba a fannonin aikin gona da kauyuka da manoma zai karu kusa da 30%

cri

Bisa labarin da jaridar People's Daily ta kasar Sin ta bayar a ran 7 ga wata, an ce, bisa shirin da aka tsara, a shekarar 2008, gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin za ta kebe kudin Sin yuan biliyan 2.07 daga baitulmali domin aikin gona da kauyuka da manoma. Wannan adadi ya karu kusa da kashi 30 cikin kashi dari bisa na shekarar 2007.

A jihar Tibet, yawan makiyaya da manoma ya kai kashi 80 daga cikin kashi dari daga cikin dukkan mutane miliyan 2 da dubu dari 8. A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, kyautata zaman rayuwar manoma da makiyaya da kara su kudin shiga nauyin farko ne da ke bisa wuyan gwamnatin jihar lokacin da take neman raya tattalin arziki da zaman al'umma na jihar.

Bisa shirin da aka tsara, ya zuwa shekara ta 2010, yawan makiyaya da manoma wadanda za su iya kwana a cikin sabbin gidaje masu inganci zai kai kashi 80 daga kashi dari bisa na dukkan makiyaya da manoma na jihar. A waje daya kuma, za a samar da cikakkun ayyukan yau da kullum, kamar su wutar lantarki da ruwan sha mai tsabta da hanyoyin mota da sadarwa da talibijin da rediyo da gidan waya a kowane kauye. (Sanusi Chen)