Ran 6 ga wata da dare, agogon wurin, an gama aikin mika wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin London na kasar Britaniya, daga baya kuma an isar da wutar yular a birnin Paris na kasar Faransa cikin jirgin saman musamman.
London tasha ta hudu ce da ake gudanar da aikin mika wutar yula a kasashen waje. Aka fara aikin mika wutar yular ne daga filin wasan motsa jiki na Wembley dake arewa maso yammacin birnin daga misalin karfe 10 da rabi na ran 6 ga wata, agogon wurin, wutar yular ta ketare unguwanni 10 na birnin London, tsawon hanyar mika wutar yular ya kai wajen kilomita 50, kuma aka kashe wajen awa 8 ana yin aikin, wato hanyar mika wutar yula a London ya fi sauran biranen kasashen waje tsawo, gaba daya masu mika wutar yula 80 sun shiga aikin.
Kodayake a ran nan, an yi kankara mai laushi mai tsanani a London, amma mutanen birnin dubbai sun je tituna domin taba zuwan wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ban da wannan kuma, aka shirya bikin taya murna iri daban daban a wuraren da wutar yular ta isa. Firayin ministan kasar Britaniya Gordon Brown ya kalli aikin a bakin kofar fadarsa dake titin Downing, gimbiya Anne ita ma ta halarci aikin taya murnar da aka shirya a wurin karshe na aikin. (Jamila Zhou)
|