
yau 6 ga wata, an fara mika wutar wasannin Olympics ta Beijing a birnin London.

London ya kasance zango na hudu da aka yada a kan hanyar mika wutar wasannin Olympics a kasashen ketare. Za a shafe tsawon awoyi 8 da rabi ana mika wutar, kuma tsawon hanyar da za a bi zai kai kilomita 50, wanda zai kasance hanya mafi tsawo wajen mika wutar wasannin Olympics ta Beijing a kasashen ketare. An fara mika wutar wasannin Olympics ta Beijing daga filin wasan Wembley da ke arewa maso yammacin birnin London, kuma gaba daya akwai masu mika wutar 80.
Bayan da aka kawo karshen mika wutar a birnin London, za a tashi zuwa birnin Paris, babban birnin kasar Faransa, don ci gaba da mika wutar. (Lubabatu)
|