
Firaministan Birtaniya, Gordon Brown ya sake jaddada a ran 5 ga wata cewa, Birtaniya ba za ta kaurace wa wasannin Olympics na Beijing ba.
Brown ya bayyana a Watford cewa, zai halarci wasannin Olympics na Beijing kamar yadda sauran mutane masu dimbin yawa za su yi.
An ce, a lokacin da wutar wasannin Olympics ta Beijing ta ratsa titin Downing a ran 6 ga wata, Mr.Brown zai yi kallon bikin mika wutar a kofar fadarsa.(Lubabatu)
|