Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-06 18:59:48    
Ministar kula da harkokin wasannin Olympics ta Birtaniya ta yi maraba da zuwan wutar wasannin Olympics a birnin London

cri

A ranar 5 ga wata da dare, wutar wasannin Olympics ta Beijing ta isa birnin London, kuma ministar kular da harkokin wasannin Olympics ta kasar Birtaniya, Tessa Jowell ta je filin jirgin sama na Heathrow, don maraba da wutar.

A yayin da take hira da manema labarai a filin jirgin sama, Madam Jowell ta ce, tana fatan mika wutar wasannin Olympics ta Beijing a birnin London da za a yi zai kasance wani biki na yada manufar wasannin Olympics da kuma biki ne domin 'yan wasa da za su shiga wasannin Olympics, haka kuma wani biki na hada kan kasashe daban daban a karkashin manufar wasannin Olympics.

Birnin Beijing zai karbi bakunci gudanar da wasannin Olympics a watan Agusta na shekarar da muke ciki, a yayin da London zai gudanar da wasannin a shekarar 2012. Madam Jowell ta ce, ya kasance da huldar musamman a tsakanin biranen Beijing da London, kuma tana farin ciki da hada gwiwa da kwamitin kula da wasannin Olympics na Beijing.(Lubabatu)