Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-06 18:59:05    
Wutar wasannin Olympics ta Beijing ta isa birnin London

cri
A ranar 5 ga wata da dare, da misalin karfe 7 da minti 25, agogon wurin, jirgin saman da ke dauke da wutar wasannin Olympics ta Beijing ta isa filin jirgin sama na Heathrow da ke birnin London, babban birnin kasar Birtaniya.

London ya kasance zango na hudu da aka yada a kan hanyar mika wutar wasannin Olympics a kasashen ketare. Za a fara mika wutar wasannin Olympics na Beijing daga filin wasan Wembley da ke arewa maso yammacin birnin London, sa'an nan, za a ratsa unguwanni 10 na London, kuma za a isa filin Peninsular da ke Greenwich na gabashin London.

Tsawon hanyar da za a bi wajen mika wutar a birnin London zai kai kimanin kilomita 50, kuma za a shafe tsawon awoyi 8 ana mika wutar, wanda zai kasance hanya mafi tsawo da za a bi wajen mika wutar wasannin Olympics a kasashen ketare.

A lokacin kuma, firaministan kasar Birtaniya, Gordon Brown da Gimbiya Anne za su hallara a gun bikin mika wutar.(Lubabatu)