Ran 5 ga wata, a birnin St.Petersburg, wanda girmansa ya zama na biyu a kasar Rasha, an sami nasarar mikawa wutar wasannin Olympic ta Beijing.
Birnin St.Petersburg zango ne ta uku a kan hanyar da ake bi wajen mikawa wutar wasannin Olympic ta Beijing a ketare. An dauki misalin sa'o'i 5 da rabi wajen mikawa wutar, tsawon hanyar da aka bi St.Petersburg ya kai misalin kilomita 20. An fara mikawa wutar daga babban filin Nasara, kuma an kammala mikawa wutar a babban filin da ke gaban Fadar Lokacin Sanyi.
A wannan rana, mutane kimanin dubu dari 7 sun yi maraba da wutar wasannin Olympic ta Beijing a titunan birnin.
Bayan birnin St.Petersburg, za a isar wutar wasannin Olympic ta Beijing a birnin London, hedkwatar kasar Birtaniya, wanda zai shirya gasar wasannin Olympic ta lokacin zafi a shekarar 2012.(Tasallah)
|