Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-05 17:27:32    
An soma mika wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing a Saint Petersburg

cri

A ran 5 ga wata da safe, agogon wurin, an soma mika wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing a birnin Saint Peterburg, birni mafi girma na biyu a kasar Rasha. Madam Galena Zybina wadda ta taba samun lambar zinariya a gun gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta zama mutumiyar farko da ta rike da wutar yola ta tashi daga Filin Nasara.

An labarta cewa, duk tsawon hanyar mika wutar yola a birnin Saint Peterburg ya kai kimanin kilomita 20, inda mutane 80 za su rike da wutar yola domin sauke nauyin da ke bisa wuyansu. Bayan isowar wutar yola a filin da ke gaban Fadar Lokacin Sanyi, za a kunna takunyar ajiye wannan wuta mai tsarki, kuma za a shirya wani kasaitaccen shagalin taya murna.

Birnin Saint Peterburg na kasar Rasha zango na uku ne a kan hanyar mika wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing a duk fadin duniya. (Sanusi Chen)