Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-05 16:49:50    
Tsohon ministan wasannin motsa jiki na Faransa ya goyi bayan wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing

cri
A ran 4 ga wata, Mr. Jean Francois Lamour, tsohon ministan wasannin motsa jiki na Faransa wanda ya taba samun lambar zinariya ta wasan takobi a gun gasar wasannin motsa jiki ta Olympic har sau 2 ya bayyana a birnin Paris, cewar yana goyon bayan gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing, kuma ya ki dukkan matakan kin halartar gasar wasannin motsa jiki ta Olympic.

A gun wani taron manema labaru da kungiyoyin 'yan kasuwa na kasar Sin da Turai suka shirya, Mr. Lamour ya ce, "tsohon shugaba Juan Antonio Samaranch da Jacques Rogge shugaba na yanzu na kwamitin Oympic na kasa da kasa dukkansu sun taba bayyana cewa, suna fatan za a iya shirya wata kasaitaciyar gasar wasannin motsa jiki ta Oympic a birnin Beijing. Ina kuma da irin wannan fata cikin sahihanci."

A waje daya kuma, Mr. Lamour ya zirgi wasu 'yan siyasa da mutane masu kare hakkin dan Adam na Faransa domin suna kokarin jawo hankulan kafofin watsa labaru da jama'a ta hanyar kin amincewa da gasar wasannin motsa jiki ta Olympic. Ya nemi jama'a da su ki yarda da a dauki matakan kin amincewa da gasar wasannin motsa jiki ta Olympic, kuma ya yi kira ga 'yan wasannin motsa jiki na Faransa da su halarci gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing kamar yadda ya kamata. (Sanusi Chen)