Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-04 20:15:35    
Hadaddiyar kungiyar addinin Buddha ta kasar Sin ta yi tir da tashe-tashen hankula a Lhasa da sauran wurare

cri
Ran 4 ga wata, hadaddiyar kungiyar addinin Buddha ta kasar Sin ta ba da wani bayani mai lakabi haka 'ya kamata a ji tausayin mutane a matsayin mai bin addinin Buddha' a cikin jaridar Guangming ta kasar Sin, inda ta yi tir da tashe-tashen hankula na rashin imani da suka faru a kwanan baya a birnin Lhasa na jihar Tibet da sauran wurare.

Bayanin ya bayyana cewa, an ta da tashe-tashen hankulan ne domin neman ta da rikici da lalata gasar wasannin Olympics ta Beijing. Sun riga sun yi sanaddiyar mutuwar mutane fiye da 10 da babbar hasarar dukiyoyi, haka kuma sun kawo wa mazauna wuraren illa a zukatansu. Tsirarun masu bin addinin Buddha sun sa hannu cikin tashe-tashen hankulan, sun saba wa dokokin kasar da kuma ka'idojin addinin Buddha, shi ya sa tilas ne su tuba da abubuwan da suka yi da kuma neman gafara. Kazalika kuma, hadaddiyar kungiyar addinin Buddha ta kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan nuna wa gwamnatin Sin goyon baya da ta dauki wajababbun matakai bisa dokoki domin kwantar da kura, tana kuma goyon bayan yanke hukunci kan masu laifuffuka bisa dokoki, haka kuma tana goyon bayan matakan kiyaye kwanciyar hankali a zaman al'ummar kasa da dokokin kasar da babbar moriyar al'ummomi.(Tasallah)