A kwanan baya, an wallafa littafi mai suna "Karya da Gaskiya" a nan kasar Sin. Dakin sayar da litattafai na Sanlian da ke karkashin jagorancin kamfanin dab'i na kasar Sin ne ya tsara wannan littafi.
A cikin wannan littafi, an yi amfani da dimbin hakikanan abubuwa domin bankado labaru da shirye-shirye marasa gaskiya da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka bayar kan matsalar nuna karfin tuwo mai tsanani da aka yi a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa na jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A cikin wannan shiri, an bayyana tarihi da al'adu da addinai na Tibet da dalilin da ya sa aka samu batun Tibet. A waje daya kuma, akwai wasu ilmomin Tibet a cikin wannan littafi. (Sanusi Chen)
|