Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-04 19:58:56    
Birnin Beijing yana dauke da wutar yula ta gasar wasannin Olympic

cri

Masu sauraro, kamar yadda kuka sani, ran 30 ga watan Maris na bana, aka yi gagarumin bikin mika wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Athens wato babban birnin kasar Greece, a gun bikin, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing Liu Qi ya dauki wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008 daga hannun shugaban kwamitin gasar wasannin Olympic na kasar Greece Minos Kyriakou. Ran 31 ga wata, wutar yula mai ma'anar halin gasar wasannin Olympic ta sauka birnin Beijing. A cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku bayani kan wannan.

Ran 30 ga wata da yamma, agogon wurin kasar Greece, shahararriyar 'yar wasa daga kasar Greece Pigi Devetzi ta yi gudu ta shiga filin wasan motsa jiki na Athens tare da wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing, daga baya kuma ta kunna kwanon wutar yula dake cikin filin. Wannan ya alamanta cewa, an riga an kammala aikin mika wutar yula da aka shafe mako guda ana yinsa a cikin yankin kasar Greece, daga baya kuma za a mika wutar yular nan ga kasa mai shirya wannan zama na gasar wasannin Olympic wato kasar Sin a hukunce.

Kafin wannan wato ran 29 ga watan Maris, kungiyar wakilai masu halartar bikin mika wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing wadda ke karkashin jagorancin mamban hukumar siyasa ta tsakiya ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma sakataren birnin Beijing wanda shi ne shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing Liu Qi ta riga ta sauka a birnin Athens, kuma a shirye suke domin tarye wutar yula.

A gun bikin mika wutar yula da aka shirya a ran 30 ga watan Maris, Liu Qi ya bayyana cewa: "Wutar yula za ta sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar Sin da dukkan jama'ar kasashen duniya baki daya, kuma za ta zaga duk fadin kasar Sin, har za ta hau kan dutsen Everest , halin Olympic shi ne sakamakon wayin kan dan adam, wutar yula ita ce alamar zaman lafiya da zumunta, ko shakka babu aikin mika wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing wanda burinsa shi ne tabbatar da yawo mai zaman jituwa zai ci cikakkiyar nasara!"

A watan Agusta na bana, za a shirya zama ta 29 ta gasar wasannin Olympic a birnin Beijing na kasar Sin, shi ya sa, a madadin gwamnatin kasar Sin da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, Liu Qi ya gayyace aminai daga kasashen duniya baki daya da su zo birnin Beijing, ya ce:  "Muna maraba da aminai daga kasar Greece da sauran kasashen duniya da su zo birnin Beijing domin shiga gasar wasannin Olympic, muna fatan jama'ar kasar Greece da jama'ar kasashen duniya daban daban za su yi kokari tare da mu domin shirya wani gaggarumin bikin wasannin motsa jiki da al'adu, ta haka kuma za a kara fahimtar juna da cudanya tsakanin jama'ar kasashen duniya baki daya. "

A tsakiyar filin wasa, mai dauke da tartsatsin wuta Maria Nafpliotou ta kunna wutar yula daga kwanon wutar yula, kuma ta mika wa shugaban kwamitin gasar wasannin Olympic ta kasar Greece Kyriakou, daga baya Kyriakou ya mika wa Liu Qi wutar yula, Liu Qi kuwa ya ajiye tartsatsin wutar a cikin wani akwatin musamman, kuma ya yi murmushi ya nuna wa manyan baki da 'yan kallo tartsatsin wutar. A karshe dai, za a isar da tartsatsin wutar zuwa birnin Beijing a ran 31 ga wata. Daga ran 1 ga watan Afrilu, za a fara aikin mika wutar yula a duk fadin duniya daga Beijing, a ran 8 ga watan Agusta da dare kuwa, wutar yula za ta sauka a wurin shirya bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma za a kunna wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a nan. (Jamila Zhou)