A kwanakin baya a wani kauye na garin Linzhou na birnin Lhasa, manema labaru ya ga Madam Amaiciren wadda shekarunta ya kai 117, mutum mafi tsohuwa da ke Tibet. Tana zauna a yadin gidanta domin jin dadin haskan rana da ke tudun Tibet.
Gidan Madam Amaiciren shi ne wani gini mai benaye biyu wanda ke da murabin mita kusan 400, a karshen shekarar bara, gwamnati da kamfannoni da ke wurin sun ba da kudi domin ginawa.
Bisa labarin da muka samu, an ce, tun daga shekarar 2006, an aiwatar da "shirin gina gidajen kwana" a jihar Tibet, ana son yin kokari domin tabbatar da kashi 80 cikin 100 na manoma da makiyayan Tibet za su shiga sababbin gidajen kwana. Ya zuwa yanzu, akwai manoma da makiyayan Tibet kamar dubu 300 sun riga sun sami sababbin gidajen kwana.
A cikin tsawon lokacin rabin karnin da ya wuce, gwamnatin kasar Sin tana kokarin sa kaimi ga bunkasuwar ayyukan kiwon lafiya a jihar Tibet.
Yanzu, akwai wurare dabam daban fiye da 1700 inda ake iya aiwatar da ayyukan addini, yanzu akwai sufi fiye da dubu 46 suna zama a cikin gidajen ibada, yawan mutane masu bin adinin Budda da suka tafi jihar Tibet domin yin addu'a ya kai fiye da miliyan a ko wace shekara.
Mutanen jihar Tibet sun nuna cewa, a cikin yawan shekaru da suka wuce, suna jin dadin zaman rayuwa, da kwanciyar hankali, da zaman jituwa sosai, kuma wannan ne fatansu mafi girma a nan gaba. Wasu mutane masu laifuffuka sun bata zaman jituwa, da kyakkyawan halin da ake ciki, wannan ya wulakanta kyakkyawan fata na mutanen zaman al'ummomi dabam daban na jihar Tibet.
|