Hukumar kula da harkokin jama'a ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta bayar da labari cewa, tun daga watan Maris da ya gabata, hukumomin gwamnatin jihar Tibet za su tallafawa otel-otel da dakunan abinci da kamfanonin kasuwanci da sauran 'yan kasuwa masu zaman kansu wadanda suka samu hasara a cikin matsalar nuna karfin tuwo mai tsanani da aka yi a ran 14 ga watan Maris domin tabbatar da zaman rayuwarsu na yau da kullum.
Mr. Xu Jianzhong, mataimakin direktan hukumar kula da harkokin jama'ar jihar Tibet ya bayyana cewa, za a tallafawa 'yan kasuwa a fannonin tallafin zaman rayuwar yau da kullum da na jiyya, wato za a samar da wasu kudade ga 'yan kasuwa wadanda ba su iya tabbatar da zaman rayuwarsu ba, kuma za a samar da taimako ga wadanda suke neman aikin jiyya a asibiti. (Sanusi Chen)
|