Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-04 17:06:46    
Babban bankin kasar Sin da kudin kasar Sin

cri

A wannan mako za mu amsa tambayoyin da malam Sanusi Isah Dankaba, mazaunin garin Keffi, jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya, da kuma malam Alhassan Juma, wanda ya zo daga jihar Gombe tarayyar Nijeriya, suka yi mana. A cikin wasikarsa, malam Sanusi Isah Dankaba ya ce, people's bank of china, shi ne babban banki tsakiya na gwamnatin kasar Sin, ko shi ne yake da alhakin kula da duk wata harka ta kudi a kasar Sin? Bayan haka ina son in san ko wannan banki shi ne yake kula da harkar kudi a yankunan Taiwan da Hongkong da Macao? Sa'an nan, malam Alhassan Juma ya ce, don Allah ina so ku gaya mini naira nawa ne yuan daya? Kuma mene ne ainihin sunan kudin kasar Sin yuan ne ko remimbi? To, domin amsa tambayoyin, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari mu dan fadakar da ku a kan harkar kudi ta kasar Sin.

Masu sauraro, bankin jama'ar kasar Sin, ko kuma People's Bank of China a Turance, ya kafu ne a ranar 1 ga watan Disamba na shekarar 1948. sa'an nan a watan Nuwamba na shekarar 1983, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yanke shawarar danka wa bankin ikon tafiyar da harkokin kudi na kasar Sin a matsayin babban bankin kasar. Daga baya, a ran 18 ga watan Maris na shekarar 1995, aka zartas da "dokar bankin jama'ar jamhuriyar jama'ar Sin" a gun taro a karo na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 8, wato ke nan aka tabbatar da matsayin bankin jama'ar kasar Sin na babban bankin kasar Sin ta hanyar kafa doka.

Bisa bunkasuwar tsarin tattalin arzikin kasuwanci na gurguzu na kasar Sin, a matsayinsa na babban bankin kasar Sin, bankin jama'ar kasar Sin na kara taka gaggarumar rawa a wajen ba da jagoranci daga manyan fannoni. Sa'an nan, dokar bankin jama'ar jamhuriyar jama'ar Sin da aka gyara a gun taro na shida na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 10 a shekarar 2003 ta kuma kayyade cewa, muhimman ayyukan da bankin jama'ar kasar Sin ke gudanarwa sun hada da tsara dokoki da ka'idojin da abin ya shafa da kyautata ka'idojin hukumomin kudi da tsara manufofin kudi da aiwatar da su da sa ido a kan kasuwannin kudaden musanya da kasuwannin zinariya. Sa'an nan, bankin yana kuma daukar nauyin kiyaye kwanciyar hankalin kasa a fannin harkokin kudi da tsara manufar darajar musanyar kudin Sin da kaddamar da kudaden Sin da gudanar da harkokin baitulmali da yin hasashen tattalin arziki. Har wa yau kuma, bankin yana ba da jagoranci kan aikin yaki da halamtar da kazamin kudi da kuma gudanar da harkokin kudi a tsakanin Sin da kasashen waje. Game da tambayar ko bankin jama'ar kasar Sin yake kulawa da harkar kudi ta Taiwan da Hongkong da Macao, to, amsa shi ne ba ya kulawa da harkokinsu, kuma wadannan yankuna uku suna da kudadensu na kansu da suka sha bamban da kudin da ake amfani da babban yankin kasar Sin. Bisa manufar mulki daya amma tsarin mulki guda biyu, bayan da Sin ta komo da Hongkong da Macao a karkashin mulkinta bi da bi a shekarar 1997 da 1999, Hongkong da Macao suna da ikon cin gashin kansu na gudanar da tsarin kudinsu, wato ke nan suna kaddamar da kudadensu na kansu, kuma suna da hukumomin da ke kulawa da harkokin kudaden.

Yanzu bari mu juya mu amsa tambayar malam Alhassan Juma. Ka ce, shin ainihin sunan kudin Sin shi ne yuan ko Renminbi, to amsa shi ne, Renmibi, wato ba Yuan ba ne, kuma kamar yadda muka ambata a baya, bankin jama'ar kasar Sin shi ne yake kulawa da kudin Sin, wato yadda za a tsara kudin da kuma kaddamar da shi. To, watakila wadanda ke sauraronmu a kullum su kan ji a cikin labaranmu cewa, kudin Sin yuan kaza da kaza, kuma yanzu suna shakkar mene ne Yuan kuma? To, bari in muku bayani. Kamar yadda kudaden Nijeriya suke, wato akwai Naira, akwai kobo, akwai sule, akwai sisi, kudaden Sin ma haka yake. Wato akwai Yuan da Jiao da Fen, kuma Yuan daya ya zo daidai da Jiao 10, a yayin da Jiao daya ya tashi daya da Fen 10. Sa'an nan, kwatankwacin kudin Sin yuan da kudin Nijeriya wato Naira, ya kai kimanin 15 zuwa 17.(Lubabatu)