Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-04 17:06:08    
'Yan sandan kasar Sin sun gano wasu makamai lokacin da suke binciken matsalar da ta auku a ran 14 ga watan Maris

cri
A ran 3 ga wata, ofishin kakakin ma'aikatar tsaron lafiyar jama'ar Sin ya bayar da labari cewa, 'yan sandan kasar Sin sun gano wasu makamai lokacin da suke binciken matsalar nuna karfin tuwo da ta auku a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa na jihar Tibet.

Bayan da aka ta da tashin hankali a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa na jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, bisa labarun da jama'a da wasu masu bin addinin Buddha suka gabatar musu, 'yan sandan jihar Tibet da na lardin Sichuan da na Qinghai da na Gansu sun yi gano wasu makamai a wasu dakunan ibada da abin ya shafa. Wadannan makamai sun kunshi bindigogi iri iri 185 tare da kananan harsashi dubu 14 da dari 3 da 67 tare da wukake 2139 da aka kayyade da a yi amfani da su da bom kilo 3862 da harsashi guda 19360 da za su iya fashewa.

A waje daya kuma, 'yan sandan kasar Sin sun gano dimbin takardu iri daban-daban da suke yayata "neman 'yanci kan Tibet".

A cikin matsalar nuna karfin tuwo mai tsanani da tsirarrun masu laifuffuka suka yi ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa na jihar Tibet, an kashe fararen hula 18 da ba su ji ba su gani ba tare da ji wa mutane 382 raunuka.An kuma kone kantuna da gidajen jama'a da yawa.(Sanusi Chen)