Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-04 15:59:40    
Wutar wasannin Olympics na Beijing ta isa birnin Saint Petersburg

cri

Ran 4 ga wata da sassafe da karfe 3 da rabi bisa agogon wurin, jirgin musamman da ke daukae da wutar wasannin Olympics na Beijing ya isa filin jirgin sama na Pulkovo da ke Saint Petersburg birni mafi girma na biyu na kasar Rasha.

A ran 5 ga wata da safe da karfe 10 da rabi bisa agogoin wurin, za a fara mika wutar yola ta wasannin Olympic ta Beijing a birnin Saint Petersburg wadda ta zama zango na uku na ayyukan mi?/ka wutar yola a duniya.

Yanzu, an riga an tabbatar da hanyar mika wutar yola. Za a fara mika wutar yola daga filin Nasara da ke kudancin birnin, kuma za a ratsa cibiyar birnin bisa titunan Moscow da Voznesenskiy, kuma za a shige ta kogin Neva, bayan an wuce fadar soja ta Peter and Paul da jirgin ruwan yawo na "Aurora", za a fara mika wutar yola zuwa kudu, a karshe za a sauka filin Zimniy Dvorec da ke kudancin bankin kogin Neva, tsayin hanyar mika wutar ya kai kimanin kilomita 20, Mutane 80 za su shiga harkar mika wutar yola