Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-03 20:37:56    
Kasar Sin tana fatan bayar da gudummowarta ga bunkasuwar wasannin Olympics

cri
A ran 3 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Jiang Yu ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin da kuma jama'ar Sin suna fatan za su iya yada ruhun Olympics ta shirya gasar wasannin Olympics, ta yadda za su iya bayar da gudummowarsu kan sa kaimi ga bunkasuwar wasannin Olympics.

A 'yan kwanakin nan da suka gabata, tsohon shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Juan Antonio Samaranch ya yi kira ga kasashen duniya da su tsagaita nuna adawa da gasar wasannin Olympics ta Beijing. Lokacin da take amsa tambayar da aka yi mata, Madam Jiang ta bayyana cewa, har kullum jami'an kwamitin wasannin Olympics na duniya suna gudanar da ayyuka bisa kundin tsarin wasannin Olympics. Lokacin da kasar Sin ke shirya gasar wasannin Olympics, kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing da kuma kwamitin wasannin Olympics na duniya sun hada kansu sosai.

Ban da wannan kuma Madam Jiang ta jaddada cewa, gasar wasannin Olympics katsaitacciyar gasa ce ta dukkan jama'ar duniya, haka kuma ita ce muhimmin wuri da jama'ar kasashe daban daban suke kara zumunci da cudanya da kuma hadin kai tsakaninsu.(Kande Gao)