Ran 3 ga wata, jaridar Global Times da aka buga a nan Beijing ta wallafi wani bayani da cewa, abubuwan gaskiya suna raunana mutuncin kafofin yada labaru na yammacin duniya da suke nuna wa Dalai Lama goyon baya da kuma daure wa karya gindi.
Bayanin ya kara da cewa, a kwanan baya, wasu masu amfani da yanar gizo ta Internet sun nuna cewa, hoton da Dalai Lama ya yi amfani da shi domin cin zarafin sojojin kasar Sin da cewa, wai sun nuna kamar masu bin addinin Buddha, wani hoto ne da aka dauka kafin shekarar 2003. Wasu kuma sun nuna abubuwan shaida cewa, dalilin da ya sa sojojin Sin da ke cikin hoton suke rike da tufafin masu bin addinin Buddha a hannu shi ne domin su nuna wasan kwaikwayo a wurin a lokacin can. Wasu masu amfani da Internet sun rubuta ra'ayoyinsu da cewa, wannan hoto ya zama abun shaida ne da ya iya tono ainihin burin Dalai Lama, wato neman ta da rikici a jihar Tibet.
Lian Xiangmin, wani manazarci da ke aiki a cibiyar nazarin ilmin jihar Tibet ta kasar Sin ya gaya wa wakilin jaridar Global Times cewa, Dalai Lama ya gwanance wajen kago karya bisa tunanin mutanen yammacin duniya, ta haka ya iya kawo wa rukuninsa riba. Sa'an nan kuma, ko kusa kasashen yammacin duniya ba su gano ainihin halin da jihar Tibet ke ciki ba. A idanunsu, ko da yake Dalai Lama ya sha yin karya, amma ba zai kawo musu illa ba, a maimakon haka, sun iya yin amfani da Dalai Lama domin raunana saurin bunkasuwar kasar Sin.
Duk da haka, bayan aukuwar tashe-tashen hankula a birnin Lhasa a ran 14 ga watan Maris, abubuwan gaskiya sun raunana mutuncin kafofin yada labaru na yammacin duniya da suke nuna wa Dalai Lama goyon baya da kuma daure wa karya gindi, har ma wasu mutanen da ke goyon bayan Dalai Lama sun ji tsoro da cewa, in irin wadannan tashe-tashen hankula sun tono yunkurin siyasa na rukunin Dalai Lama, to, Dalai Lama zai rasa harsashi a yammacin duniya.(Tasallah)
|