Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-03 18:59:31    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin (18)

cri

---Nada sabon suna ga wani kauye ya zama matsala. Mutane fiye da hamsin a wani kauye na gundumar Wenchang na lardin Hainan na kasar Sin ba su iya samun takardun shaidun matsayinsu wato ID cards ba sabo da aka nada sabon suna ga kauyen da suke zama,domin a cikin na'ura mai kwakwalwa babu wata kalma da suke so wadda za ta alamanta za su samu wadata,haka kuma mutane da dama suna samu matsaloli kamar su ba su iya samun takardun shaidu na aure,da samun aikin yi da ziyara da kuma daidaita batutuwa dangane da dukiyoyinsu.

----Maza ma'aikatan hukuma da yawa suna fama da ciwon prostatitis.Bisa labarin da aka samu,an ce kashi 55 bisa dari na maza ma'aikatan hukuma na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin suna fama da cutar prostatitis bayan da aka yi musu bincike.An samu wannan sakamako ne bayan da aka yi wa ma'aikatan hukuma 8,199 binciken lafiya tsakanin shekara ta 2005 da ta shekara ta 2006.Mataimakin darektan hukumar kiwo lafiya ta lardin Guangdong Mr Liao Xinbo ya fadi haka.Ya kuma ce kashi 34 bisa dari suna fama da matsalar hawan jini,sauran kashi 17 bisa dari suna fama da matsalar hanta.An ce matsin da ayyuka masu yawa suka kawo da kuma cin abinci fiye da ake bukata su ne dalilin da ya sa maza ma'aikatan hukuma suna fama da cutar prostatitis.

---An tsare wata mata mai kwadayi sabo da ta kwaci kudin da danuwansa ya samu daga wajen tambola. Kwanakin baya an tsare wata mata sabo da ta kwaci abin da danuwanta ya samu da darajarsa ya kai kudin Sin Yuan miliyan daya a birnin Zhengzhou na lardin Henan na kasar Sin.Sunan matar shi ne Zhang.Danuwanta ya samu kudin Sin Yuan miliyan biyar a cikin tambola da aka yi a shekarar bara,ya ba ko wane 'yanuwansa hudu kudin Sin rabin miliyan.Amma wannan mataa ta fi kwadaita ta kuma saci wani miliyan daban.daga baya aka gabatar da ita a gaban kotu a farkon wannan shekarar da muke ciki.Yayin da mata Zhang ta kin karbar hukuncin da kotun ta yanke mata sai ta mayar da kudin ga danuwanta.kotun ta tsare ta.

----Mafarauta na musamman sun daidaita matsalar da namun daji suka kawo. Gwamnatin birnin Yichang na cikin shirin kafa wata kungiyar musamman domin farautar namun daji sama da 1200 da suka kawo matsala ga manoma masu yawa da shuke shukensu.Mafarauta na musamman sun samu horaswa ta yaki da namun daji a wannan birni na lardin Hubei.Yawn namun daji na karuwa a cikin shekarun baya.Wannan ya kawo barna mai tsananni ga dankalin turawa da shinkafa da gyada da sauran shuke shuken da ake nomawa.Bisa kiyastawa da aka yi,an ce irin namun dajin da suka kawo barna sun wuce dubu ashirin a yankin Yichang.

---Wata mace ba ta so ganin likita namiji.Kwanakin baya wata mace tana so ta zuba da cikinta a birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin,da ta ga likita namiji ya shiga ya kula da ita.sai ta tafi abinta.Sunan macen shi ne An.Da ta shiga dakin sai ta kwanta a kan gadon tana jiran a yi mata fida.Da ta ga wani likita namiji ya shiga cikin dakin,nan da nan ta tashi daga kan gadon.Sai asibitin ya sake shirin ya aika wata likita mace domin kula da mace An. An ce likita namiji nada shekaru 26 da haihuwa,macen nada shekaru 27 da haihuwa.Dukkansu ba su ji dadi kan halin da suka samu kansu a ciki ba.Wannan batu ba daya ne kawai a asibiti.Irin batun da aka fi gani shi a asibitoci da yawa na kasar Sin.

---Wani saurayi ya ci tara sabo da ya shiga wata liyafa ba tare da izni ba.Kwanakin baya wani saurayi a birnin Baoding na lardin Hebei sabo da ya shiga wata liyafa da aka shirya domin bikin aure.Yayin da sabbin ma'aurata biyu suka daga kwaf suna masa godiya kan shiga liyafar sun ga alamun shan banban daga wannan mutum,sun shiga shakku da kirawo 'yan sanda.Da 'yan sanda suka yi masa tambaya,ya amsa laifinsa da cewa sau da yawa ya shiga burtun baki sa'an nan ya halarci liyafar da aka shirya domin bukukuwan aure.

---rigar barawo ta jawo hankalin masu gadi.An tsare wani mutum a gidan 'yan sanda sabo da ya yanke wayoyin da tsawonsu ya wuce mita dari hudu a wani wurin gina babban gini na birnin Shijiazhuang na lardin Hebei.Yayin da mutminnan ya fita daga kofa masu gadi sun ga mutumin nan ya sa babbar riga fiye da kima,suna tsammani watakila akwai wani abu a ciki.sai sun bukace shi da ya tube babbar riga.Da ya tube,ashe wayoyi ne na nannade a jikinsa.nauyinsu ya kai kilo ashirin,sai a tsare shi.

---An yanke hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan wakafi kan wani mutum da ya sayar da tabar jabu.An yanke hukuncin dauri na shekaru bakwai a gidan wakafi kan wani mutum a yankin Chaoyang na birnin Beijing sabo da ya tanadi tabar jabun da darajarsu ta kai kudin Sin miliyan 7.3 a gidansa.Sunan mutumin shi ne Shi Bi.A farkon wannan shekara,'yan sanda suka kama shi sabo da ya tuki wata motar dake dauke da taba.Daga baya an gano duk taban dake cikin motar na jabu ne.'Yan sanda sun kai samame a gidansa inda suka gano taban jabu masu yawan gaske.

Jama'a masu sauraro,kun dai saurari sabon shirinmu na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin.Wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau,mun gode muku saboda kuka saurarenmu,ku huta lafiya.(Ali)