Samun gidajen kwana, wani muhimmin abu ne ga jama'ar kasar Sin a cikin zaman rayuwarsu, tun 'yan shekarun da suka wuce, kyautatuwar halin gidaje na jama'ar kasar Sin, ita ma ta zama wani batun da ke jawo hankulan mutane sosai. A gun taro na zaman farko na majalisar wakilai ta jama'ar kasar Sin a karo na 10, wakiliyarmu ta kai ziyara ga wasu 'yan majalisar wakilai musulmi da suka halarci taron, dukkansu sun bayyana cewa, tun bayan da aka yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, halin gidajen kwana da jama'a musulmi na kasar Sin ke ciki, ya samu kyautatuwa sosai. A cikin shirinmu na yau kuma, za mu yi muku bayani kan wannan.
Malam Bai Shangcheng, 'dan majalisar wakilai daga wani yanki mai duwatsu na jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui, ya gabatar da halin gidaje da farar hula na yammacin kasar Sin ke ciki, kafin aka yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Ya ce, "A da, halin gidaje na farar hula da ke yankinmu mai duwatsu ba ya da kyau, dukkanmu mun zauna a kogunan dutse, kuma kullum kogunan dutse sun yi yayyo."
Kogunan dutse da Bai Shangcheng ya ambata, su ne gidajen kwana na farar hula da ke kauyuka a yammacin kasar Sin, a cikin dogon lokacin kafin aka yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar, farar hula da yawa sun yi zama a cikin kananan kogunan dutse kamar haka. A yammacin kasar Sin a lokacin, ko da mazaunan birane su kan yi zama a gidaje masu hawa daya da aka gina da bulo, kuma kullum 'yan iyali uku ko hudu, har ma zuriyoyi guda uku suna zama tare.
A lokacin da kuma, halin gidajen kwana na birnin Beijing ya fi kyau bisa na sauran shiyyoyi, amma duk da haka, yawancin mutane sun yi zama a gidaje masu hawa daya, wadanda suka yi zama a gine-gine kuma, sun yi zama a gine-ginen da aka kira "Tong Zi Lou". Abin musamman na gine-gine irin haka shi ne, ko wani gida na da daki daya kawai, dakin dafa abinci, da bayan gida duk na jama'a ne, babu dabara sai dai 'yan iyalin su yi dukkan ayyuka a wannan daki. 'Yar majalisar wakilai madam Wang Xiaoke daga birnin Beijing, ta taba zama a gini kamar haka cikin dogon lokaci, kuma ba ta iya mantawa da wani lamarin da iyalinta ke karbar baki daga kasashen waje ba. "A lokacin, babana wani malami ne na sashen Sinanci na wata jami'a, saboda haka, kullum yana gudanar da wasu ayyukan hadin gwiwa tare da kasashen duniya. Wata rana, wasu baki daga kasashen ketare sun zo gidanmu, don tattauna wasu ayyuka, amma saboda ba mu da sauran dakuna, don haka sai su tsuguna kan gado. A ganinsu, dakin kwana daki ne na asiri, bai kamata a yi shisshigi ba, amma a lokacin ba mu da dakin zanawa ba."
Wang Xiaoke ta gaya wa wakiliyarmu cewa, fatanta a lokacin shi ne, samu wani gida da ke da dakin dafa abinci da bayan gida na kansu.
Yanzu, wani sakamakon da manufar yin gyare gyare da bude kofa ga kasashen waje, da kuma samun bunkasuwar tattalin arziki suka haddasa kai tsaye shi ne, jama'ar kasar Sin sun samu kyautattuwa a fannin gidajen kwana. 'Dan majalisar wakilai daga jihar Ningxia, malam Bai Shangcheng ya ce, "Tun bayan da aka yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, jiharmu mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta yi gyare-gyare kan kogonan dutse, da gidaje masu hadari, a sanadiyar haka, farar hula sun kaura daga kogunan dutse, bayan haka kuma, gwamnatinmu ta bayar da taimakon kudi na kudin Sin RMB yuan dubu takwas ga ko wane iyali, ta yadda farar hula sun samu gidajensu kamar yadda ya kamata."
Bugu da kali kuma, malam Bai Shangcheng ya gayawa wakiliyarmu cewa, tun da shekaru 30 da suka wuce, ko da a cikin mafarkin da ya yi, bai taba yin zaton zai iya zama a babban gida, har ma zai iya wanka a gida nasu. "A da, na kan yi wanka a waje, yanzu ina zama a babban gida, kuma halin gidan kwana ya samu kyautattuwa sosai, na iya wanka a ko wane lokacin da nake so."
'Dan majalisar wakilai malam Abdulah Abbas, shi ne wani shehun malami na kolejin kimiyya da fasaha na rayuwa na jami'ar Xinjiang, yana shan aiki a yau da kullum. Amma, ya ce, bayan da ya koma gida a ko wace rana, muhallin gidansa mai kyau na zamani, ya kan sanya masa manta da gajiyar jikinsa. Ya ce, "Yanzu iyalinmu da ke hade da mutane hudu muna zama a wani gida mai hawa biyu da ke da fadin muraba'in kilomita sama da 150, ko wanenmu muna da dakunan kwana na kanmu, muna iya kallon talibijin, da shiga tashoshin internet a gidanmu, lallai halin zaman rayuwarmu da koyo yana da kyau sosai."
A lokacin da take ambatar sauye-sauyen titin Niujie, wato wurin da musulmi 'yan kabilar Hui ke zaune a birnin Beijing a shekaru 30 da suka wuce, 'yar majalisar Wang Xiaoke tana jin farin ciki sosai. Ta ce, "A da, babu manyan kantuna a titin Niujie, sai dai kananan kantuna, kuma dukansu sun tsofa. Yawancin gidajen kwana gidaje masu hawa daya kawai, da kyar ake iya ganin gine-gine. Yanzu, gwamnatinmu ta kafa manufofi da yawa na nuna fifiko, kuma ta kiyaye abin musamman irin al'adun kabilar Hui na gidajen kwana da ke wurin."
Ya zuwa karni na 21, mutane suna da zababbu da yawa a fannin gidajen kwana, kamar su gine-gine masu hawa da yawa, da masu hawa biyu, har ma manyan gidaje masu kayatarwa wato VILLA masu abubuwan musamman. Bisa kara matsayin zaman rayuwar jama'a, a lokacin da suke neman gidaje masu fadin muraba'I, a waje daya kuma suna neman kara kyautattuwar muhalli na gidajensu.
Daga gidaje masu hawa daya, da gine-ginen "Tong Zi Lou" a da, har zuwa manyan gine-gine, da gidaje masu hawa biyu, da kuma VILLA, musulmin kasar Sin suna jin manyan sauye-sauyen da aka samu cikin sauri da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ke haddasa, kuma suna kece raini daga sakamakon da aka samu wajen manufar. Sun yi imani cewa, za su kara jin farin ciki kan gidajen kwanansu nan gaba.
|