
Da misalin karfe 12 da minti biyar na safiyar 3 ga wata, agogon wurin, jirgin saman musamman mai lambar 'wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing' wanda ke dauke da wutar yula ya sauka a birnin Istanbul na kasar Turkey daga kasar Kazakhstan, daga nan an fara tasha ta biyu ta aikin mika wutar yula ta gasar wasannin Olympic a kasashen waje.
An fara aikin ne daga filin cocin Aya Sofya dake cibiyar birnin Istanbul, gaba daya hanyar mika wutar yula tana hada da matakai uku, tsawonta ya kai kilomita 18.8. Masu mika wutar yula 80 za su shiga aikin a birnin Istanbul, bayan an isar da wutar yular a wurin karshe, za a kunna ta kuma za a shirya gaggarumin biki domin taya murna.
An samu labari cewa, gidan telibijin TRT na kasar Turkey zai watsa labarai kan aikin mika wutar yula kai tsaye.
Ran 2 ga wata, birnin Alma-Aty, an riga an sami nasarar shirya aikin mika wutar yular gasar wasannin Olympic ta Beijing a birni mafi girma na kasar Kazakhstan. Alma-aty da Istanbul su ne muhimman birane dake kan 'hanyar jigilar da siliki' a zamanin da. Tashar gaba ta aikin mika wutar yular ita ce birnin Saint Petersburg na kasar Rasha. (Jamila Zhou)
|