Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-03 10:35:03    
Wu Bangguo ya jaddada cewa, za a gudanar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing lami lafiya

cri

Kwanakin baya, shugaban zaunannen kwamitin majaliar wakilan jama'ar duk kasar Sin Wu Bangguo ya yi rangadin aiki a birnin Beijing, inda ya jaddada cewa, dole ne mu kara kyautata aikin share fage na gasar wasannin Olympic, ta yadda za mu shirya gasar wasannin Olympic da gasar wasannin Olympic ta nakasassu masu matsayin koli da kuma masu tsarin musamman a birnin.

Wu Bangguo da 'yan rakiyarsa sun je filin wasannin motsa jiki na kasar Sin da cibiyar wasan iyo ta kasar Sin da sauran dakuna da cibiyoyin wasannin Olympic domin kara gane ayyukan share fage irin daban daban da ake yi domin gasar wasannin Olympic.

Wu Bangguo ya bayyana cewa, shirya wata gasar wasannin Olympic mai tsarin musamman shi ne burin al'ummar kasar Sin a cikin shekaru dari daya da suka shige, kuma shi ne alkawarin da dukkan jama'ar kasar Sin da yawansu ya kai miliyan 130 suke yi ga duk duniya baki daya. Dole ne bangarorin da abin ya shafa su nuna kwazo da himma domin gudanar da ayyukan share fage na mataki na karshe yadda ya kamata. (Jamila Zhou)