Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-02 20:21:53    
An raba addini da siyasa a Tibet cigaba ne da aka samu a tarihi

cri
A ran 2 ga wata, Mr. Lian Xiangmin, direktan ofishin nazarin kimiyya na cibiyar nazarin ilmin Tibet ta kasar Sin ya bayyana a birnin Beijing, cewar an raba addini da siyasa a yankin Tibet cigaba ne da aka samu a tarihi. Rukunin Dalai Lama yana son hada addini da harkokin siyasa, wannan ya saba wa ka'idar tarihi.

A gun wani taron manema labaru da ofishin yada labaru na gwamnatin kasar Sin ya shirya a wannan rana, Mr. Lian Xiangmin ya ce, a matsayin wani mai bin addini, har kullam Dalai Lama yana tafiyar da harkokin siyasa. Makasudinsa shi ne farfado da tsarin hada addini da harkokin siyasa bai daya a yankin Tibet. Mr. Lian ya kara da cewa, tabbas ne tsarin hada addini da harkokin siyasa bai daya ba zai koma yankin Tibet ba har abada. Kowane mutum wanda ke kokarin farfado da wannan tsari a yankin Tibet, tabbas ne jama'ar kabilu daban daban, ciki har da 'yan kabilar Tibet wanda suke da zama a yankin Tibet ba za su amince da shi ba. (Sanusi Chen)