Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-02 21:45:53    
Wani madugun 'yan tawayen da suka tada zaune tsaye a jihar Tibet ta kasar Sin ya amince da tunzurar da rukunin Dalai Lama ya yi musu

cri

Saurari

Jiya Talata, ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin ta kira taron watsa labaru a nan birnin Beijing, inda ta bayyana sabon halin da ake ciki dangane da binciken tarzomar da aka yi ta kai farmaki kan jama'a, da farfasa kayayyaki, da wawashe su da kuma sa wurare wuta a ran 14 ga watan jiya a birnin Lhasa, fadar gwamnatin jihar Tibet ta kasar Sin. Kakakin ma'aikatar ta ce, hukumar 'yan sanda ta birnin Lhasa ta riga ta kama wani madugun 'yan tawayen da ya shirya wannan tarzomar, ya kuma amince da laifin da ya yi na neman jawo wa al'ummar kasa baraka bisa umurnin da wani jami'in rukunin Dalai Lama ya ba shi. Bisa cikakkun abubuwan shaidun da hukumar 'yan sanda ta kasar Sin ta samu, an tabbatar da cewa, tarzomar ran 14 ga watan jiya wani kashi ne na shirin da rukunin Dalai Lama ya tsara na wai "kamfen tayar da babban boren jama'ar Tibet", makasudinsa shi ne domin haddasa rikici a kasar Sin ta hanyar daukar matakan tada zaune tsaye a jihar Tibet ta kasar.

A gun taron watsa labarun da aka shirya jiya, Malam Wu Heping, kakakin ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin ya bayyana wa kafofin watsa labaru na gida da waje misalin 100 cewa, "bayan ran 15 ga watan jiya, hukumomin tsaron jama'a sun kama wasu masu manyan laifuffuka wadanda ake zarginsu da sa hannu cikin kulla makarkashiyar tada tarzomar ran 14 ga watan jiya, wadanda kuma ke da alaka da rukunin Dalai Lamai sosai. Sa'an nan an fara gano hanyoyin da wani wai shi jami'in hukumar tsaro na rukunin Dalai Lama ke bi don tada zaune tsaye a kasar Sin. A kwanakin baya, hukumar tsaron jama'a ta birnin Lhasa ta kama wani magudun 'yan tawaye wanda ya sa hannu cikin shirin tayar da tarzomar ran 14 ga wata jiya kai tsaye, kuma ya amince da laifuffukan da suka yi na neman jawo wa al'ummar kasa baraka bisa umurnin wani jami'in rukunin Dalai Lama."

Hukumar 'yan sanda ta kasar Sin ta jaddada cewa, sabo da yanzu ana nan ana binciken tarzomar, shi ya sa bai kamata a bayyana sunan wannan madugun da ake tsare da shi a fili ba. Yanzu, hukumar tana tahumarsa bisa doka.

Malam Wu Heping ya kara da cewa, a hakika, abin na wai "kamfen tayar da babban boren jama'ar Tibet", shi ne yin amfani da damar karshe da suka samu daga wajen wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 wajen neman cim ma makarkashiyarsu ta 'yancin kan Tibet', ta yadda za su jawo wa kasar Sin baraka daga bisani. Ya ce, "makasudin abin na wai 'kamfen tayar da babban boren jama'ar Tibet' da rukunin Dalai Lama ya shirya, shi ne domin lalata kyakkyawan halin da ake ciki a kasar Sin dangane da zaman lafiya da hadin kai, da yi amfani da wasannin Olympic wajen kai wa gwamnatin kasar Sin matsi, don cim ma makarkashiyarsu ta jawo wa kasar Sin baraka. Wasannin Olympic ya gabatar da manufarsa game da shimfida zaman lafiya da kawar da yaki da tarzoma, amma 'yan a-ware wadanda rukunin Dalai Lama ke shugabanta suna neman mayar da wasannin Olympic a siyasance, sun mayar da wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 kamar damar karshe da suka samu na neman tabbatar da 'yancin kan Tibet', sun yi zafin nama wajen tsara shirin adawa da wasannin Olympic. Irin wannan ta'asar ta saba wa manufar tsarin dokoki na Olympic sosai, kuma ya shafe bakin fenti ga jama'a masu kishin zaman lafiya na dukkan duniya gaba daya."

Bisa matsayinsa na kakakin ma'aikatar tsaron jama'ar kasar Sin, Malam Wu Heping yana fatan jama'ar duniya za su tsaya kan baka ga abubuwa iri daban daban da rukunin Dalai Lama ke yi. Ya ce, "amma kullum Dalai Lama ya kan sanar da cewa, wai ya kamata a bayyana ra'ayi cikin ruwan sanyi. Amma hakikanan abubuwan da suka faru sun tabbbatar da cewa, abin na wai hanyar sassautawa da zanga-zangar zaman lafiya ba zai kulla wani abu ba, illa ya zama karyar da shi da rukuninsa suka yi. Sabo da haka muna fatan jama'ar duniya za su tsaya kan bakansu ga abubuwa iri daban daban da rukunin Dalai Lama da kungiyar 'yan a-wari masu neman 'yancin kan Tibet ke yi. Mun hakake, karya karya ce, daga bisani hakikanan abubuwa za su tono makarkashiyar da rukunin Dalai Lama ya kulla kan neman jawo wa kasar Sin baraka. (Halilu)