Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-02 17:53:13    
Jaridar "China Daily" ta buga wani bayani mai take "mene ne Dalai Lama yake son tattaunawa?"

cri
A ran 2 ga wata, jaridar China Daily ta kasar Sin ta buga wani bayani mai take "Mene ne Dalai Lama yake son tattaunawa da sunan 'yin hakikanin shawarwari'".

A cikin wannan bayani, an ce, a kwanan baya, Dalai Lama ya bayyana cewa, "bai canja matsayinsa na bin hanyar tsakiya ko kadan ba", yana fatan "shugabannin kasar Sin za su iya yim amfani da dabaru domin yin hakikanin tattaunawar zaman lafiya da 'yan Tibet". Amma wace irin hanyar tsaiya da Dalai Lama yake bi? Kuma mene ne yake samu ta hanyar yin shawarwari da gwamnatin tsakiya?

Wannan bayani ya kara da cewa, a shekarar 1987 da ta 1988, bi da bi ne Dalai Lama ya bayar da "ra'ayoyi 5 na tabbatar da zaman lafiya a Tibet" da "Sabbin ra'ayoyi 7". Bisa wadannan ra'ayoyinsa, ya bayar da matsayinsa na wai bin hanyar tsakiya. Hakikanin ma'anar wannan hanyar tsakiya ita ce gyarawa da kasa fahimtar ikon mulkin Tibet, kuma yana son musunta tsarin siyasa da ake aiwatarwa a yankin Tibet yanzu, har ma yana son nema kafa babban yankin Tebet da bai taba kasancewa a tarihi ba. Ya kuma nemi mutanen sauran kabilu da su bar babban yankin Tibet da yake son kafawa. A waje daya kuma, ya nemi a janye sojojin kasar Sin daga babban yankin Tibet da sauran sharudan da ba su dace ba. Sabo da haka, wannan bayani ya nuna cewa, wannan ba hanyar tsakiya ba ce, amma a fili ne Dalai Lama yana son neman 'yancin kan Tibet, kuma yana son ta da tashe-tashen hankali da tarzoma a kasar Sin ba tare da tangarda ba.

Bayanin ya kara da cewa, a cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta yi hakuri sosai wajen neman yin tuntubar bangaren Dalai Lama. Ko da yake rukunin Dalai Lama ya ta da tashin hankali a birnin Lhasa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sint a bayyana cewa, tana bin manufa kan Dalai Lama kamar yadda take sabawa a bayyane sosai, ba ta canja matsayinta ba. Amma lokacin da rukunin Dalai Lama yake fadin cewa yana son yin tuntubar gwamnatin tsakiya, yana shirya, kuma yana ta da tashe-tashen hankali da tarzoma. Irin wadannan matakan da yake yi suna lalata tushen yin shawarwari sosai. Idan yake da sahihanci wajen ci gaba da yin tattaunawa da gwamnatin tsakiya, ya kamata ya daina zuga da shirya ayyukan ta'addanci, kuma ya daina matakan lalata wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing, kuma ya daina matakan kebe yankin Tibet daga kasar Sin. Wannan ne babban tushe ga shawarwarin da ake so. (Sanusi Chen)