Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-02 17:10:27    
An shirya bikin nuna wasannin Cartoon na daliban Jami'o'i na kasa da kasa a birnin Beijing

cri

Kwanan baya, an shirya bikin nuna wasannin Cartoon na daliban jami'o'I na kasa da kasa a karo na biyu a jami'ar koyar da ilmin yada labarai ta kasar Sin . Bisa matsayin kasar Sin na shirya bikin nuna wasannin Cartoon na daliban jami'o'I na kasa da kasa a karo na farko ne, bikin ya zama dakalin wasanni na nuna kwarewar sabbin mutane wadanda suke da fasahar wasannin Cartoon, sa'anan kuma dakali ne na kara wa juna ilmi a tsakanin manyan mutane a kan wasannin fasahohi da yada labarai na kasar Sin, wanda ya sa kaimi ga horar da kwararrun wasannin Cartoon na kasar Sin da raya masana'antunsu.

Shugaban jami'ar koyar da ilmin yada labarai ta kasar Sin Mr Su Zhiwu ya bayyana cewa, ayyukan da aka yi a wannan gami duk domin samar da wani dakalin wasanni ga dimbin masu kishin wasannin Cartoon da fasahar yada labarai wajen yin ma'amalar tunaninsu da fasahohinsu da bayyana kwarewarsu da kuma shirya bikin tamkar yadda babbar walima da aka shrya ga daliban jami'o'I na duk duniya wajen nuna wasannin Cartoon.

Jami'ar koyar da ilmin yada labarai ta kasar Sin tana daya daga cikin jami'o'in da suke soma koyar da fasahar wasannin Cartoon da yin bincicke a kai a kasar Sin . Tun daga shekarar 2004, tana soma shiga cikin rukunin farko na sansanoni hudu na yin bincike kan aikin koyarwa bisa matsayin kasa. Daga shekarar 2006, jami'ar ta soma shirya bikin nuna wasannin Cartoon na daliban kasa da kasa a birnin Beijing don samar da wani dakalin musanya ra'ayoyi a kan fasahar wasannin Cartoon ga daliban kasashe daban daban na duniya da masanan da abin ya shafa.

Shugaban kwamitin kula da harkokin ilmi na Siggragh na kasar Amurka Mr Rick Barry ya bayyana cewa, bikin nuna wasannin Cartoon na daliban kasa da kasa ya samar wa samari dalibai wani dakalin wasanni na nuna kwarewarsu, inda aka amince da matsayin daliban da ke kwarewa sosai, wannan na da muhimmanci sosai ga aikin ba da ilmi . ya bayyana cewa, an nuna amincewa ga daliban da ke kwarewa sosai kuma suka riga suka dauki sinima, a ganina, wannan na da muhimmanci ga aikin ba da ilmi, nuna amincewa ga daliban da ke kwarewa sosai zai sa himma gare su wajen ci gaba da kago sabbin abubuwa, a sa'I daya kuma, a iya ba da taimako ga wadannan dalibai da su ci gaba da koyon ilmi.

Wata daliba ta jami'ar mai suna Shi Qianqian ta gaya wa manema labaru cewa, bikin nuna wasannin Cartoon da aka shirya a birnin Beijing ya samar wa dalibai wata tagar bayyana su, yanzu, yawancin masu shiga gasar wasannin Cartoon su ne daliban kasar Sin, za a gayyaci daliban kasashen waje da yawa don yin ma'amalar fasaha.Wannan ne abu mafi kyau ga daliban da suke koyon fasahar wasannin Cartoon a cikin jami'o'insu.

Mun sami labari cewa, a duk kasar Sin da akwai daliban da yawansu ya kai dubu 500 da suke koyon fasahar wasannin Cartoon da sauran ilmi dangane da wasannin Cartton a jami'a, wannan ya zama tushen masana'antun yin wasannin Cartoon na kasar Sin.

Wani jami'in hukumar kula da harkokin gidan rediyo da TV da sinima na kasar Sin Mr Jin Delong ya bayyana cewa, yanzu, masana'antun fitar da finafinan wasannin Cartoon sun sami makomar bunkasuwa mai kyau , ya ce:yawan wasannin Cartton da kasar Sin ta yi na kara karuwa, kuma ana ta samun nagartattun wasanni, sa'anan kuma dakalin nuan wasannin Cartoon sai kara yawa suke yi , tsarin masana'antun yin wasannin Cartoon ya sami kyautatuwa a kai a kai ba tare da katsewa ba. (Halima)