Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-02 17:03:24    
Kara samun matsin lamba a rayuwa zai kara hadarin kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini a bayyane

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "ilmin zaman rayuwa". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan cewa, Kara samun matsin lamba a rayuwa zai kara hadarin kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini a bayyane.

Bisa sabon sakamakon nazarin da kasar Amurka ta bayar, an ce, bayan afkuwar harin ta'addanci da aka kai wa kasar Amurka a ran 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001, har kullum dimbin 'yan kasar Amurka da ba su samu tasiri kai tsaye ba su ma suna jin tsoro da kuma damuwa a cikin zaman rayuwarsu, kara samun matsin lamba a rayuwa ya sa hadarinsu wajen kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini ya karu a bayyane idan an kwatanta da na sauran mutane.

Manazarta na jami'ar California ta kasar Amurka sun gudanar da bincike ga mutane 2592 na duk fadin kasar har shekaru uku bayan faruwar lamarin ta'addanci. A ciki, kashi 3.6 bisa dari daga cikinsu sun sha wahalar lamarin kai tsaye, ko su ne wadanda suka yi a idonsu, ko kuma iyalansu suna wurin faruwar lamarin. Haka kuma kashi 63.2 bisa dari daga cikinsu sun san lamarin ta talibijin, kashi 33.2 bisa dari daga cikinsu ba su taba ganin ko wane labari kan batun ba.

Daga baya kuma sun gano cewa, ko da yake mutane da yawansu ya kai 3.6 cikin dari kawai sun sha wahaloli kai tsaye a cikin lamarin ta'addanci, amma kashi 10.7 cikin dari sun mayar da martani sosai kan lamarin, kuma yawansu da aka tabbatar da cewa, sun kamu da cututtukan zuciya da hauhawar jini ya karu da kashi 53 cikin dari idan an kwatanta da sauran mutane.

Manazarta na kasar Birtaniya sun gano cewa, mutanen da su kan ji gajiya sosai wajen aiki sun fi saukin samun kiba fiye da kima, shi ya sa ya kamata mutane masu shan aiki sosai su sassauta gajiya da suke ji da kansu.

Ta yin nazari a fannin ilmin likitanci, an riga an gano cewa, irin wannan gajiya da a kan ji wajen aiki a dogon lokaci tana da nasaba da cututtukan zuciya da na sauye-sauyen halittu na jikunan bil-adama. Amma a cikin wannan nazarin da Eric Brenner da abokan aikinsa na kwalejin ilmin likitanci na jami'ar London ta kasar Birtaniya suka yi, sun gano cewa, idan gajiya da masu aikin yi suka ji ta karu, sai yiyuwar samun kiba fiye da kima gare su za ta karu.

Manazarta sun gudanar da wani bincike na tsawon shekaru 19 ga maza 6895 da kuma mata 3413 wadanda shekarunsu ya kai 35 zuwa 55 da haihuwa. A cikin binciken, wadannan mutane sun gabatar da takardun tambayoyi game da gajiyar da su kan ji wajen aiki na lokaci-lokaci. Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da wadanda suka amince da jin gajiya sosai wajen aiki a cikin takardun tambayoyi har a kalla sau uku, yiyuwar samun kiba fiye da kima gare su ta karu da kashi 73 cikin dari idan an kwatanta da wadanda ba su taba jin gajiyar aiki ba.

Sabo da haka Mr. Brenner yana ganin cewa, wannan sakamakon bincike ya samar da wata muhimmiyar shaida kan cewa, gajiya wajen aiki ita ce muhimmin dalilin da ke haddasa samun kiba fiye da kima.