Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-02 08:04:33    
Gasar guje-guje ta gasar wasannin Olympic ta zamanin da

cri

Kamar yadda kuka sani, aka shirya zama ta farko ta gasar wasannin Olympic a shekarar 1896, kuma a kwana a tashi gasar wasannin Olympic ta kara jawo hankulan mutanen kasashen duniya. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan asalin gasar wasannin Olympic ta zamanin da da gasar guje-guje ta gasar wasannin Olympic ta zamanin da.

Asalin gasar wasannin Olympic shi ne gasar wasannin Olympic ta zamanin da wadda aka shirya a tsohuwar kasar Greece a can can da wato a shekarar 776 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam. Ya zuwa shekarar 394, gaba daya aka taba shirya gasar wasannin Olympic ta zamanin da sau 293. Wurin shirya gasar wasannin Olympic ta zamanin da shi ne Olympia, wani karamin gari dake da nisan kilomita wajen 300 daga birnin Athens na yanzu, an ce, gumakan Greece su kan taru a nan, aka mayar da wurin a matsayin wurin ibada mai tsarki, kuma aka kiransa da suna 'Altis', a wurin, daga gabas zuwa yamma, tsawonsa ya kai wajen mita 200. A gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da, wasa ta farko ita ce gasar gudun mita 192. Kafin shekaru 2000, a kan wani babban dutsen dake kan tsaunin Greece, aka sassaka wata jimla kamar haka:'Idan kana son kara lafiyar jiki, idan kana son kara wayo, idan kana son kara kyan gani, sai ka je gudu. '

A gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da, kafin zama ta 14, sai wasa daya kawai, wato gasar gajeren gudu mai mita 192, kuma 'yan wasa sun yi gasa ba tare da sa riga da takalmi ba. Ya zuwa shekarar 724 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, a gun zama ta 14 ta gasar wasannin Olympic ta zamanin da, aka kara wata wasa wato gudu mai matsakaicin zango, 'yan wasa sun yi gudun mita 192 sau biyu ke nan. A shekarar 720 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, a gun zama ta 15 ta gasar, aka sake kara wata wasa wato gudu mai dogon zango, 'yan wasa sun yi gudun mita 192 sau 24, a karshe dai, tsawonsa ya kai wajen mita 4600.

A gun zama ta 65 ta gasar wasannin Olympic ta zamanin da da aka shirya a shekarar 520 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, aka kara wata wasa wato gudu mai damara, yayin da 'yan wasa ke gudu, dole ne su sa hular karfe a kansu kuma su refu gwiwarsu da fatar sa, ban da wannan kuma, suna dauke da garkuwa mai nauyi a hannun hagunsu. Saboda irin wannan gasa ta fi tsanani, kuma 'yan kallo sun fi nuna sha'awa kanta, shi ya sa gasa mai damara ta zama bikin rufe gasar wasannin Olympic, wanda ya zama zakara kuma zai zama 'dan wasa mafi nagari na Greece. (Jamila Zhou)