Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-01 21:33:48    
Rukunin Dalai Lama ya zuga shi da ta da tarzoma, a cewar wani muhimmin mai tarzoma

cri
Ran 1 ga wata, a nan Beijing, Wu Heping, kakakin ma'aikatar tsaron lafiyar al'umma ta kasar Sin ya yi karin bayani da cewa, a kwanan baya, 'yan sanda na birnin Lhasa sun kama wani muhimmin mai tarzoma da ya sa hannu da kuma shirya tashe-tashen hankula a birnin Lhasa a ran 14 ga watan Maris kai tsaye. Wannan mutum ya kulla hulda tare da wani jami'in rukunin Dalai Lama, ya kuma amince da cewa, rukunin Dalai Lama ya ba shi kwarin gwiwa da ya aikata laifin kawo baraka ga al'ummomi.

A gun taron manema labaru da aka yi, Mr. Wu ya bayyana cewa, wannan mutum ya amince da cewa, shi da rukunin Dalai Lama sun tuntubi juna ta hanyar kalmomin asiri, ya dade ya tattara aisiri a kasar Sin. Amma saboda ana tono wannan batu, shi ya sa bangaren 'yan sandan bai bayyana sunan wannan mutum ba tukuna, kuma yanzu 'yan sandan suna bin bahasin batun bisa dokoki. (Tasallah)