A ranar 31 ga watan Maris, an yi bikin bude shawarwarin Majalisar Dinkin duniya a karo na farko kan sauye-sauyen yanayin sararin samaniya a birnin Bangkok, hedkwatar kasar Thailand. Shawarwarin Majalisar Dinkin duniya da aka yi a wannan gami kan sauye-sauyen yanayin sararin samaniya shawarwarin farko ne da abin ya shafa bayan da aka zartas da taswirar tsibirin Bali a gun babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka shirya a watan Disamba na shekarar da ta shige dangane da sauye-sauyen yanayin sararin samaniya.
A gun taron da aka shirya a wannan gami, za a yi tattaunawa kan yadda za a aiwatar da taswirar tsibirnin Bali da yadda za a iya tsara shirin aiki a bayyane dangane da gudanar da shawarwarin da za a yi a nan gaba. Sa'anan kuma, taron zai yi tattaunawa kan yadda za a sa kaimi ga kasashe masu ci gaba da ke kasancewa cikin bangaren da suka sa hannu kan yarjejeniyar Protocol ta Kyoto don ci gaba da cika alkawarin rage iska mai dumi.
A gun taron, kasashe masu tasowa wadanda rukunin kasashe 77 da kasar Sin suke wakiltarsu da harshe mai zafi ne suka nemi kasashe masu wadata da su rage iska mai dumi a gaban sauran kasashe bisa ka'idar daukar nauyi tare kuma na da bambanci da aka tabbatar da ita a cikin yarjejeniyar tsarin sauye-sauyen yanayin sararin samaniya na Majalisar Dinkin duniya. A gun taron da aka yi a wannan rana, shugaban sashen ba da shugabanci ga ayyukan maganin sauye-sauyen yanayin sararin samaniya na kasar Sin Mr Su Wei ya bayyana cewa, kasashe masu wadata suna da hakki bisa wuyansu kuma suna da karfin rage fitar iska mai dumi. Ya ce, bisa rahoton kimantawa da kwamitin musamman na sauye-sauyen yanayin sararin samaniya na tsakanin gwamnatoci ya yi a karo na hudu, an bayyana cewa, a shekarar 2004, a cikin kasashe masu wadata, kowane mutum ya fitar da makwatancin iska mai guba da yawan nauyinsu ya kai ton 16.1, saboda haka ya kamata kasashe masu wadata su dauki nauyi bisa wuyansu su ci gaba da rage iska mai dumi, kuma suna da karfin yin hakan. Kasar Sin tana goyon bayan rahoton kimantawa wato IPCC da aka yi a karo na hudu , a kalla kasashe masu wadata su rage iska mai dumi kuma mai guba da yawansa ya kai kashi 25 zuwa kashi 40 bisa na shekarar 1990 bayan shekarar 2012.
Game da cewar wasu kasashe masu wadata sun gabatar da batun , ya kamata a mayar da nauyin iska mai dumi kuma mai guba da za a fitar a shekarar 1990 bisa na shekarar 2005 , sakataren sakatariyar yarjejeniyar tsarin sauye-sauyen yanayin sararin samaniya na Majalisar Dinkin duniya Mr Yvo De Boer ya bayyana cewa, a ganina, yin magana kan batun tamkar yadda na yi magana kan wata doguwar tafiya wato Marathon ne, wato da akwai inda za a soma tashi da gudu, amma, ba a san tsawon gudun da za a yi ba. A gun taron da muka shirya, za a yi tattaunawa kan nauyi nawa ne da kasashe daban daban za su so su rage fitar da iska mai dumi kuma mai guba.idan wasu kasashe ba su so su rage iska mai dumi kuma mai guba bisa nauyin da aka fitar a shekarar 1990 ba, to makasudinsu shi ne don gyara inda aka soma tashin gudun Marathon.
A gun taron da aka yi a wannan rana, wakiliyar internet na maganin sauye-sauyen yanayin sararin samaniya ta kungiya ba ta gwamnati ba ta yi kirari da kakausar murya cewa, ya kamata kasashe daban daban su dauki matakai da sauri don rage fitar da iska mai dumi kuma mai guba a hakika, don sassauta dumama yanayin sararin samaniya. Ta bayyana cewa, bai kamata ba ku jira zuwan gobe, ya kamata ku yi aiki tun daga yau. Ya kamata ku yi tunawa da cewa, halin da ake ciki na kara wa yanayin sararin samaniya dumi a duk duniya zai kai matsayin koli a shekaru goma masu zuwa, ku ba ku da kowane dalilin da za ku jinkirtar da aikin, sai ku yi aiki nan da nan da kuma ci gaba da rage fitar da iska mai dumi kuma mai guba.(Halima)
|