A ran 1 ga wata, bangaren 'yan sanda na kasar Sin ya bayyana a birnin Beijing, cewa a cikin al'amuran aikata laifuffuka na tashe-tashen hankali da aka yi a birnin Lhasa a ran 14 ga watan Maris, fararen hula 18 sun mutu, kuma an tabbatar da asalin mutane 16 daga cikinsu. Daga cikin fararen hula da suka rasu, akwai 'yan kabilar Han yayin da akwai 'yan kabilar Tibet.
Kafin wannan, hukumar 'yan sanda ta birnin Lhasa ta bayar da cewa, a cikin wadannan mutane 18, 12 daga cikinsu sun rasa rayukansu ne sakamakon tada gobarar da aka yi har sau hudu da gangan.
Sauran mutane hudu da aka tabbatar da asalinsu ba da jimawa ba maza ne, kuma biyu daga cikinsu matasa ne na kabilar Tibet, daya saurayi ne na kabilar Han da ya zo daga lardin Gansu, dayan kuma tsoho ne na kabilar Han mai shekaru 60 da haihuwa da ya zo daga lardin Sichuan.(Kande Gao)
|