Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-01 20:10:29    
Kada wasu mutanen kasashen Turai su nuna bambanci ga hakkin 'dan Adam na Tibet

cri

Ran 1 ga wata, kamfanin dilancin watsa labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar da wani sharho cewa,, kada wasu mutanen kasashen Turai su "nuna bambanci" ga hakkin 'dan Adam na Tibet.

A cikin wannan sharho, an ce, a cikin dogon lokacin baya, kullum wasu mutanen kasashen Turai sun nuna bambanci, sun zargi halin hakkin 'dan Adam da ake ciki a Tibet bisa ma'auninsu ba iri daya ba. Bayan aka sami al'amarin ta da manyan laifuffuka masu tsanani sosai a cikin birnin Lhasa na jihar Tibet, sun bayar da labarai masu yawa wadanda suka karya abin gaskiya, kuma ba su dauke nauyin da ke bisa wuyansu ba. Wasu mutanen da ke da nufin musamman sun ce manyan laifuffuka masu tsananin da mutane masu tada hankula suka yi su ne wai "zamga-zanga cikin lumana", kuma sun ce ayyukan kiyaye rayuka da kayayyakin jama'a da gwamnatin kasar Sin ta yi wai "zalunci".