Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-01 19:13:52    
Burin wani makiyayi dan kabilar Zang malam Danzhencuo,

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu ci gaba da ziyararmu a lardin Qinghai. A shekarun nan da suka wuce, hukumomin kasar Sin na matakai daban daban da jama'ar Sin sun tattara karfin mutane da kuma zuba kudi kan kyautata da kiyaye muhalli a wajen, shi ya sa muhallin halittu na wannan lardi na samun kyautatuwa a bayyane.

A lardin Qinghai da ke arewa maso yammacin kasar Sin, akwai wani kyakkyawan tabki mai suna Qinghai, a bakinsa kuma, an tsugunar da 'yan kabilar Zang, sun ciyar da kansu da kiwon sa da tumaki daga zuriya zuwa zuriya. A can da, a ko ina makiyaya 'yan kabilar Zang suna kiwon sa da tumaki. Amma duk da haka, bayan da wakilinmu ya isa lardin, bai ga wani shanu ko kuma wata tunkiya ba. Me ya sa haka? Malam Danzhencuo, wani makiyayi na wurin ya gaya mana cewa,

'Na sayar da dukkan sa da tumaki da na kiwo. Gwamnatinmu ta aiwatar da manufar maido da makiyayai zuwa tabki, tana kokarin kiyaye tabkin Qinghai da kuma kiyaye muhallin halittu.'

Iyalin Danzhencuo na zama a gundumar Haiyan da ke da nisan kilomita 30 a tsakaninta da tabkin Qinghai a arewa maso gabas, inda aka fi samun yawan 'yan kabilar Zang.

Ga shi, karen da Danzhencuo ke kiwo na maraba da mu da kukansa. Danzhencuo da iyalinsa na zama a cikin bukkar da makiyayi 'yar kabilar Zang kan zama. A kewayen gidansa akwai manyan tsaunuka, an kuma shimfida wata mikakkiyar hanyar mota a gaban gidansa. Malam Danzhencuo namiji ne sosai, kuma makiyayi ne sosai. Bayan da muka shiga gidansa, mun zauna a kan jan kafet din ulu tare, mai gida ya samar mana abin sha da abinci masu sigar musamman ta kabilar Zang. Muna cin abinci tare, muna hira tare. Wakilinmu ya ji mamaki da cewa, ina ra'ayin wannan makiyayi bayan da ya sayar da dukkan shanu da tumukinsa? Danzhencuo yana murmushi, ya amsa cewa,

'Na yi begensu kwarai bayan da na sayar da su ba da jimawa ba. Dukkansu na fara kiwonsu a lokacin da suke kanana. Bayan rabin shekara ko fiye, na sami sauki kadan. Yanzu a wani lokaci, na taba ganinsu a mafarkina.'

A shekarun nan da suka wuce, saboda dumamar yanayi a duk duniya, matsalar kwararar rairayi ta tsananta sosai a filin ciyayi da ke dab da tabkin Qinghai, wanda ke daya daga cikin manyan fadamomi guda 7 a duniya, shi ya sa zurfin ruwan tabkin na ta raguwa, irin wannan mummunan sakamako zai kawo illa ga sauye-sauyen yanayi a kasar Sin har ma duk duniya kai tsaye. Shi ya sa don kiyaye daidaiton muhallin halittu a tabkin Qinghai, gwamnatin Sin ta tsai da kudurin maido da makiyayai zuwa tabki a wuraren da ke dab da tabkin Qinghai a shekarar 2003 don kiyaye filin ciyayi a kusa da tabkin da kuma hana zaizayewar kasa. Saboda haka, kamar yadda sauran makiyaya a kauyensa suke, Danzhencuo ya rasa abin da zai yi, sai sayar da shanu da tumakinsa.

A lokacin da muke hira, uwar gida ta kawo mana giyar da 'yan kabilar Zang suka yi daga hatsi. Ta gaya mana cewa,

'Kafin maido da makiyayai zuwa tabki, mun taba kiwon tumaki fiye da 400 da shanu fiye da 400. Mun sami kudin Sin yuan dubu 10 ko fiye daga wajen sayar da su a kowace shekara, zamanmu na ba yabo ba fallasa. Amma mun sayar da su dukka, yaya makomarmu? Mu 'yan kananan kabilu mun ciyar da kanmu da sayar da shanu da tumaki daga zuriya zuwa zuriya. A lokacin can, a ganina, ba za mu ci gaba da zamanmu ba.'

Bayan da muka sha kofunan giya, Danzhencuo ya kara son yin magana da mu. Ya ce, bayan da aka aiwatar da manufar maido da makiyayai zuwa tabki ba da dadewa ba, kamar yadda matarsa take, kauyawa da yawa ba su fahimci irin wannan manufa ba. Amma ya amince da manufar gwamnatin kasar. A ganinsa, irin wannan manufa za ta kawo alheri a nan gaba. Ya ce,

'A da, garinmu na da kyan gani sosai. Shudin sararin sama da farin gajimare da filin ciyayi kowa da kowa ke kishin wannan kyan karkara. Amma yau da shekaru da dama da suka wuce, kwararar rairayi ta tsananta a filin ciyayi a wurinmu. Sa da tumaki ba su da wurin cin ciyayi. Kwarran manyan tsaunuka sun kasance busasshe. In ba a kyautata irin wannan hali ba, to, balle ma sa da tumaki, har ma ba mu da wurin kwana. Shi ya sa muna son maido da makiyayai zuwa tabki, ta haka yaranmu da jikanmu za su iya ganin shudin sararin sama da farin gajimare da kuma filin ciyayi a nan gaba.'

Amma yaya iyalin Danzhencuo da sauran makiyaya suke ci gaba da zamansu? Uwar gida Yingsheng mai hikima ta gano cewa, motoci masu daukar fasinjoji kan wuce a kan hanyar mota da ke gaban gidanta, don taka, ta fito da wata dabara, ta nemi a raya da gidanta zuwa wurin da masu yawon shakatawa ke iya fahimtar rayuwa da al'adun kabilar Zang. Hukumar kauyensu ta goyi bayan shirin Yingsheng, ba ta bata lokaci ba, sai ta taimake ta shirya ayyukan da abin ya shafa. Sa'an nan kuma, hukumar wurin ta soke wa iyalin Yingsheng harajin ciniki, ta kuma ba su kyautar bukka don karbar baki. Ta haka, iyalin Danzhencuo ya kafa otel din musamman na farko a kauyensu, inda masu yawon shakatawa suke iya fahimtar rayuwa da al'adun kabilar Zang.

Danzhencuo ya ci gaba da cewa, bayan da gwamnatin Sin ta aiwatar da manufar maido da makiyayai zuwa tabki, ta fito da yawan manufofi domin bai wa makiyaya fifiko, ta kuma bayar da kos iri daban daban ba tare da biyan kudi ba. Ta haka, suna kara jin dadin zaman rayuwarsu, in an kwatanta shi da na da. A kauyen da Danzhencuo ke zama, wasu sun ci rani a sauran wurare, wasu kuma sun koyi tukin mota sun yi cinikin jigilar kayayyaki, wasu kuwa sun yi cinikin yawon shakatawa, kamar yadda iyalin Danzhencuo ya yi.

Game da cinikinsa, Danzhecuo ya ji zumudi, ya ce,

'Raya gidana zuwa irin wannan otel din musamman dabara ce mai kyau ainun. Masu yawon shakatawa da suka zo daga tsakiyar kasar suna sha'awar kawo wurinmu ziyara domin shan kindirmo da kuma madara. Kasuwa kan ci a watan Yuli da na Agusta na kowace shekara. A watan jiya kacal, mun sami kudin Sin yuan dubu 4 ko fiye.'

Yingsheng ta gaya mana cewa, yanzu ko da yake ba su ci gaba da kiwon sa da tumaki ba, amma abin farin ciki shi ne, danta da 'yarta sun kawo karshen zamansu na kiwon sa da tumaki, sun je karatu, suna koyon ilmi kamar yadda yara 'yan birane suke yi. Dadin dadawa kuma, gwamnatin Sin ta yafe musu da sauran yara kamarsu kudin makaranta. Ko da yake suna karatu a yanzu, amma a wasu lokuta, sun tuna da lokacin da suke kiwon sa da tumaki a filin ciyayi da kuma wakar da suke rera a lokacin can.

Tare da wakar yaransa, Danzhencuo ya gaya mana cewa, a cikin zuciyarsa, yana da buri cikin dogon lokaci. Ya ce,

'Yanzu muna yin cinikin yawon shakatawa, gwamnatinmu ta ba mu fifiko da yawa, haka kuma, mu kan karbi masu yawon shakatawa masu yawa, muna fi shan alewa. Amma in an maido da dasa bishiyoyi da ciyayi a manyan tsaunuka a wurinmu, muhalli ya sami kyautatuwa, to, ina fatan in ci gaba da kiwon sa da tumaki, in sayi sa da tumaki dari 5 ko dari 6, in kara samun kudi, ta haka yarana za su shiga jami'a.'(Tasallah)