Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-01 19:09:06    
Ya kamata a magance kamuwa da cututtukan jijiyoyin zuciya da na kwakwalwa a sassafe

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. Yanzu yawan Sinawa da ke kamuwa da cututtukan jijiyoyin zuciya da na kwakwalwa ya kai kimanin miliyan 200, kuma yawan mutanen da suka mutu sakamakon cututtukan a ko wace shekara ya zarce miliyan biyu. Nazarin likitanci ya bayyana cewa, sassafe lokaci ne da aka fi saukin kamuwa da cututtukan jijiyoyin zuciya da na kwakwalwa, haka kuma kullum likitoci na dakunan gaggawa na asibitoci sun fi shan aiki a wannan lokaci. To a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku yadda ya kamata a magance kamuwa da cututtukan jijiyoyin zuciya da na kwakwalwa a sassafe.

"an dauko wannan mutum ne da karfe 4 na safe, wanda ya kamu da cutar toshewar jijiyoyin zuciya ta gaggawa, sabo da cutar tana da tsanani, kuma shekarunsa da haihuwa ya yi yawa, shi ya sa za a sanya shi cikin dakin sa ido."

"an dauko wannan mutum da karfe 6 na safe, kirjinsa ya ji zafi, amma yanzu zafin ya sassauta, har yanzu ba a iya tabbatar da cutar da yake kamuwa ba."

Wakilinmu ya samu wannan amo ne a cikin asibitin Anzhen na birnin Beijing a wata rana da sassafe. A wannan rana da safe kawai, an dauko mutane da dama zuwa asibitin sakamakon kamuwa da cututtukan jijiyoyin zuciya da na kwakwalwa. Bayan da aka yi masa jiyya, Mr. Wang da ya kamu da cutar ya gaya wa wakilinmu cewa, "lokacin da nake kamuwa da cutar zuciya, na kan yi gumi da yawa, ban iya yin numfashi kamar yadda ya kamata ba, kuma kirjina ya kan yi zafi sosai, kuma na kan ji haka da sassafe."

Don me aka fi saukin kamuwa da cututtukan jijiyoyin zuciya da na kwakwalwa da sassafe? Kwararru suna ganin cewa, dalilin ya sa shi ne sabo da hakan yana da nasaba da wasu al'adun jikin dan Adam, kamar kullum jikin dan Adam ya kan bukaci yawan iskar oxygen da sassafe, ta haka za a kara nauyin da ke bisa zuciya, kuma wasu abubuwa marasa kyau da ake ji a rai su kan karu da sassafe. Furofesa Madam Zhang Weijun ta cibiyar nazari kan ilmin likitanci na kiwon lafiyar tsoffi ta kasar Sin ta bayyana cewa, "lokacin da aka tashi da sassafe, za a samu hauhawar jini da yawan sinadarin adrenalin, shi ya sa ya kamata mutanen da ke da hauhawar jini su mai da hankali sosai a wannan lokaci."

Ban da wannan kuma furofesa Hong Zhaoguang, kwararre ne a fannin cututtukan jijiyoyin zuciya da na kwakwalwa na asibitin Anzhen na birnin Beijing ya bayyana cewa, idan ana son magance wannan lokaci mai hadari wato sassafe, dole ne a tsaya tsayin daka kan "rabin minti daya guda uku". Kuma ya kara da cewa, "bayan da mutane masu kamuwa da cututtukan jijiyoyin zuciya da na kwakwalwa suka farka a sassafe, kada su tashi nan da nan, sai su kwance a kalla rabin minti daya. Kuma bayan da suka tashi, ya fi kyau su zauna a kan gado har rabin minti daya. Daga baya kuma su dage kafafunsu har rabin minti daya. Bayan da wadannan rabin minti daya guda uku, za su iya yin sauran abubuwa."

Ban da wannan kuma furofesa Hong ya ce, idan mutanen da suka kamu da cututtukan jijiyoyin zuciya da na kwakwalwa suna iya mai da hankulansu a kan wasu dalilai, kamar tarihin kakaninsu, da hauhawar jini, da kitse fiye da kima da ke cikin jini, da cutar sukari, da shan taba, da samun kiba fiye da kima, da rashin motsa jiki, da shan giya fiye da kima da dai sauransu, to za a iya rage rabin yiyuwar kamuwa da cututtukan.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ce ke shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Kande Gao)